Tawassuli (Kamun Kafa)4
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4
Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Tarihin Kamun kafa Da Bayin Allah Tsarkaka Tarihi a bayyane yana nuna cewa tun kafin zuwan musulunci mutane masu kadaita Allah sun kasance suna Kamun kafa da wadanda suke ganin suna da matsayi a wurin Allah, sannan kuma sakamakon tsarkin fidirarsu su suna ganin wannan aiki wani aiki ne wanda yake mai kyau. A nan zamu yi nuni da wasu daga cikinsu: 1-Abdul Mutallib da kamun kafa da Muhammad (s.a.w) a lokacin da yake shan nono, tsananin fari ya mamaye Makka da kewayenta, sai Abdul mutallib ya dauki jikansa mai shan nono ya daga sama, sannan ya roki Allah ruwan sama, har ana cewa mashahuriyar wakar Abu Dalib ya yi ta ne dangane da haka wacce take cewa: Fuska mai haske wacce gizagizai suka yi ruwa dominta, wacce sakamakon haka ne marayu da mata gwagware suka samu mafaka. 2-Abu Dalib da kamun kafa da Manzo a lokacin da yake saurayi Kamar abin da ya faru lokacin Abdul mutallib a lokacin shugabancin Abu Dalib ma ya sake faruwa, sakamakon haka ne sai kuraishawa suka zo wajensa suka kawo masa kuka a kan fari da rashin ruwa da ake ciki, Sai Abu Dalib ya yanke shawara a inda ya roki Allah da ya saukar musu da ruwa tare da kamun kafa da dan dan'uwansa Muhammad wanda yake karamin yaro ne a wannan lokaci. Sai ya kama hannun Manzo ya jingina bayansa ga dakin ka'aba, wani lokaci yana nuni da wannan yaro wani lokaci kuwa yana nuni da sama, wato Ubangiji albarkacin wannan yaro ka saukar mana da rahamarka. Ba tare da tsawaita lokaci ba, sai hadari ya mamaye garin Makka da kewayanta, sai koramu da tabkuna suka cika makil da ruwa . 3-Sallar rokon ruwa tare dakananan yara da tsofaffi A cikin ladubban sallar rokon ruwa ana cewa ya fi dacewa masu sallar rokon ruwa su fita tare dakananan yara da tsofi, har wasu ma suna cewa a tafi tare da dabbobi ma wajen wannan sallar rokon ruwa. Manufar kuwa zuwa dakananan yara marasa laifi da tsofaffi raunana da dabbobi wadanda ba su magana shi ne, domin suna cewa idan su ba su cancanci rahamar Ubangiji ba sakamakon zunubbansu . Ya Ubangiji wadannan kananan yara mararsa laifi, da tsofaffi raunana, da dabbobi wadanda ba su iya magana, sun cancanci rahamarka. Ya Ubangiji albarkacinsu ka aiko mana da rahamarka! Ya uabngiji! Mai lambu saboda itaciya guda daya yake ban ruwa, amma sakamakon haka sai ciyawu ma su samu! Wannan yana nuna mana cewa tun kafin zuwan musulunci mutane a dabi'ance sun kasance suna kamun kafa da abubuwan da suka cancanci rahamar Allah, don neman biyan bukatunsu, kuma da musulunci ya zo ya tabbatar musu da hakan. 4-Khalifa na biyu yana kamun kafa da Ammin Manzo (s.a.w) Bukhari a cikin sahih dinsa yana ruwaito cewa Umar Bn khattab a lokacin fari da tsananin rashin ruwan sama ya kasance yana kamun kafa da Abbas dan Abdul Mutallib domin su samu ruwan sama, ga abin da yake cewa: Ya Allah muna muna rokonka albarkacin annabimmu ka shayar da mu ruwa, ya Allah muna kamun kafa zuwa gareka da ammin annabimmu ka shayar da mu sai su sha! Dangane da danganen wannan hadisi kuwa babu sauran wata magana domin kuwa sahih bukhari karbabbe ne a wajen 'yan Sunna, saboda haka magana kawai ta rage wajen ma'anarsa. Duk lokacin da aka bai wa wani balarabe wannan hadisi wanda a cikin zuciyarsa bai hadu da wani sabani ba zai ce: Khalifa na biyu ya kasance yana kamun kafa ne da ammin Manzo domin Allah madaukaki ta albarkacinsa ya aiko da ruwan sama ya shayar da su saura su samu. Wannan addu'a kuwa tana nufin cewa ya Allah idan harm u ba mu cancanci ka yi ruwa saboda mu ba, to albarkacin ammin Manzo domin alakar da suke da ita a tsakaninsu ka aiko mana da ruwan sama. Saboda haka idan a nan ana nufin kamun kafa da wani mutum ne, to kamun kafa da Manzo ya fi komai dacewa, domin kuwa Abbas ya samu darajarsa ne daga Manzo (s.a.w) saboda haka me ya sa a nan ya bar Manzo ya yi kamun kafa da Abbas, wannan shi ne abin tambaya a nan? Amsar wannan kuwa shi ne a wajen rokon ruwa ana kamun kafa ne da wadanda masu rokon ruwa suke daya da shi wajen bukatr ruwan, kamar kananan yara da tsofaffi, ta yadda zasu motsa rahamar Ubangiji, su ce ya Allah idan mu ba mu cancanci wannan ba to wadannan kananan yara da tsofi sun cancanta ka aiko saboda su. Saboda haka wannan ya cancanta ga ammin Manzo wanda ya kasance yana raye a wannan lokaci, ba wai Manzo ba domin kuwa shi a wannan lokaci ya bar duniya kuma halin da suke ciki ya bambanta. Wadanda suke sabani a kan halascin kamun kafa ko tawassuli da manyan bayin Allah suna fito-na-fito ne da wannan hadisi, saboda haka ko ta halin kaka suna kokari ne suga sun karkatar da ma'anarsa, suna cewa abin da khalifa yake nufi a nan yana kamun kafa ne da addu'ar Abbas, ba wai yana kamun kafa ba ne da shi kansa Abbas ko wani matsayi na shi. Wannan tawili kuwa ta fuskoki daban-daban ba zai inganta ba: Na farko: Sallar rokon ruwa da addu'ar, umar ne ya gabatar da su ba Abbas ba, saboda haka a nan babu magana a kan addu'ar Abbas. Abin da kuwa yake tabbatar mana da cewa wannan addu'a umar ne ya yi ta ba Abbas ba, lafazin da ya zo a cikin addu'ar kamar haka: Ya Allah mun kasance muna kamun kafa da Manzo ka shayar da mu, yanzu muna kamun kafa da ammin Manzo ka shayar da mu, a wannan lokaci sai ruwa ya sauka aka shayar da su. Saboda haka wannan yana nuna cewa wanda ya gabatar da wannan shiri tun daga farko har karshe khalifa ne, ba wai Abbas ammin Manzo ba, ballantana Umar ya yi kamun kafa da addu'arsa. Na biyu: Dalili na biyu shi ne a cikin babin da wannan addu'a ta zo yana magana ne a kan neman mutane daga shigaba don ya roka musu ruwan sama yayin da aka samu fari da rashin ruwan sama. Wannan yana nuna cewa mutane su ne suka nemi khalifa da ya roka musu ruwan sama, shi kuma ya amsa musu rokn da suka yi masa. Saboda haka a cikin wannan al'amari matsayin Abbas shi ne lokacin da umar yake addu'a ya yi nuni da shi inda yake cewa: "Ya Allah muna kamun kafa da ammin Manzo ka shayar da mu" Na uku: Ibn Asir ya yi bayani yadda aka gabatar da wannan salla da addu'ar rokon ruwa, yana cewa Umar ya kasance yana nuni da Abbas yana cewa: "Wallahi wannan shi ne tsani zuwa ga Allah kuma mai tsayi a wurinsa" . Ya kasance yana rokon Allah ruwa a cikin wannan hali. Don haka kamun kafa ya kasance da shi kansa Abbas ne ba da addu'arsa ba. Ibn Hajar Askalani (ya rasu 852) a wajen sharhin wannan hadisi yana rubuta cewa: dangane da abin da ya faru da Abbas yana nuna mana yadda ya halatta mutum ya yi kamun kafa da mutanen kwarai da iyalan gidan Manzo don samu ruwan sama . A karshen wannan Bahasi zamu yi tunatarwa da cewa, Tawassuli ko kamun kafa da addu'a wacce take kowa ya aminta da wannan, wani nau'i ne na kamun kafa da wanda yake addu'a sakamakon matsayi da girma da yake da shi a wajen Allah. Domin kuwa idan da mai yin addu'ar ba shi da wani matsayin na musamman a kan abin da ya shafi tsarkin ruhi, sam addu'arsa ba zata iya zama mai tasiri ba. Kamun kafar Masu Tsarki Da Matsayi A Cikin Ruwaya Ya zo a cikin ruwayoyi da dama na AhlusSunna dangane da kamun kafa da manyan bayin Allah tsarkaka, amma abin mamaki a nan shi ne masu sabani da wannan abu duk da cewa suna ganin wadannan ruwayoyi har yanzu suna ci gaba da wannan fito na fito nasu, a nan masu wannan akida suna koyi ne da Ibn Taimiyya ba suna koyi da gaskiya ba ne, idan da ba suna yanke hukunci ba ne tun kafin su ga dalilai tabbas da ba zasu dage ba a kan wannan akida tasu ba. A nan zamu kawo wasu daga cikinsu: 1-Atiyya Aufi ya ruwaito daga Abu Sa'idul Kudri yana cewamanzo ya ce: duk wanda ya fito daga gidansa da nufin zai je masallaci ya yi salla idan ya karanta wannan addu'ar rahamar Ubangiji zata lullube shi, sannan mala'iku da yawa zasu yi masa addu'a su nema masa gafara a wajen Allah. Wannan addu'a kuwa ita ce: "Allahumma inni as'aluka bi hakkis Sa'ilina alaika, wa as'aluka bihakki mashai haza, Fa inni lam akhruj ashran wala batran wala rayyan wala sum'a, innama kharajtu itka'a saktik wabtiga'a mardhatika, an tu'izani minan nar, wa an tagfira zunubi, innahu la yagfiruz zunuba illa ant" Wato, ya Ubangiji! Ina rokonka don matsayin masu rokonka, ina rokonka da matsayin wannan tafiya tawa, kuma ban fito ba don jin dadi ko saboda riya in nuna wa wasu mutane, ya Allah na fito ne domin tserewa fushinka da azabarka da neman yardarka, ya Allah ka tseratar da ni daga wuta, kuma ka gafarta mini zunubbaina don babu mai gafarta zunubbai sai kai. Wannan hadisi dangane da ma'anar a kan abin da muke magana a kan shi na kamun kafa da masu matsayi da tsarki a fili yake. Sannan sanad ko danganen wannan hadisi ingantacce ne domin kuwa dukkan maruwaitan wannan hadisi an amince da su, sai kawai mutum guda wanda dole mu yi bayani a kansa, wannan kuwa shi ne Atiyya Aufi. Masana ruwaya sun yi hukuncin da ya dace a kansa: Abu Hatim yana rubuta cewa: Ana iya rubuta hadisinsa. Ibn Mu'in yana cewa: Mutumin kirki ne. Ibn Hajar yana cewa: Mai gaskiya ne. Ibn Adi yana cewa: Ya kasance yana ruwaito hadisi daga mutanen kirki. Ibn Sa'ad yana cewa: Hajaj ya rubuta wa wani daga cikin hakimansa mai suna Muhammad Bn Kasim takarda cewa: Ka kama Atiyya, sannan ka bijiro masa da zagin Ali ya kara da cewa shi mutum ne amintacce sannan hadisansa ingantattu ne. Idan har ma wasu sun kasance suna sukarsa laifinsa bai wuce shi'anci ba, shi'an da ma'anarsa shi ne son Ali da 'ya'yansa (a.s) Sannan yanayin wannan hadisi yana tabbatar mana cewa maganar ma'asumi ce, sannan makamantan wannan hadisi suna da yawa a musulunci. Kamun kafa Da Manzo Da Annabawan Da Suka Gabata Dabarani a cikin mu'ujam dinsa, ya ruwaito hadisi tare da dangane daga Anass Bn Malik yana cewa: lokacin da Fadima bnt Asad ta rasu, Manzo ya halarci gadon mutuwarta, sai ya ce: Ya Allah ka yi wa mamata ta biyu rahama, kin kasance kina jin yunwa kina kosar da ni, kin kasance kina rasa sutura kina suturta ni, kinkasance kina kin cin abin ci mai dadi ni kuwa ki ba ni mai dadi, ba ki da wata manufa a cikin wannan aiki sai neman yardar Allah. Sai Manzo (s.a.w) ya ba da umarni da a yi mata wanka sau uku, sannan ya ciro rigarsa ya ce a yi mata likkafani da ita, sannan ku yi mata lahadu (wani nau'in kabari ne) da umurnin manzon Allah, sannan shi da kansa ya shiga cikin kabarin, ya debo kasar lahadun da hannayansa, bayan ya gama wannan aiki, sai ya kwanta a cikin kabarin ya ce: Ya Allah wanda yake kashewa kuma shi a raye yake ba ya mutuwa, ka gafarta wa uwata Fadima bnt Asad, ya Allah ka fahimtar da ita hujjarka, Ya Allah ka yalwata kabrinta albakarcin girman manzonka da manzanninka da suka gabata, kamar yadda kake mafi jin kan masu Jin kai . Wannan hadisi yana bayyanar da matsayin mahaifiyar Imam Ali (a.s) kamar yadda wannan hadisi yake nuna cewa ana iya kamun kafa da masu tsarki. Kawai abin da zai jawo hankalin masu sabani a cikin wannan al'amari shi ne, wani maruwaici guda daya mai suna ruh Bn Salah, duk da cewa Ibn Habban da Hakim Nishaburi wadanda suka kasance babu kamarsu a cikin ilimin hadisi a zamaninsu sun yi bayani a kan cewa wannan mutum amintacce ne. A nan zamu takaita dangane da kawo hadisai AhlusSunna, duk da cewa akwai ruwayoyi da dama da suka fi haka a kan wannan magana, amma dangane da ruwayoyin da suka zo daga Ahlul baiti (a.s) danagane da wannan nau'i na kamun kafa suna da yawan gaske, ta yadda suna da yawan gaske a cikin addu'o'in Amirul mumininna da Husain da addu'o'in Imam Zainul abidin (a.s) Imam Husain (a.s) a cikin addua'r arfa ga abin da yake cewa: Ya Allah muna fuskantarka a cikin wannan dare wanda ka daukaka shi ka kuma girmama shi, Allah muna kamun kafa da Manzonka Muhammad wanda shi ne fiyayyen halittarka sannan amintaccenka wajen kai wahayi. A nan zamu yi nuni dangane da wasu kalu bale a takaice: Kalu balanta Da Amsoshinsu Kalu bale na farko: shi ne, wannan nau;in tawassuli ko kamun kafa bai kasance ba a lokacin sahabbai da tabia'i? Amsa: Ta fuskar ka'idoji na ilimi, aikin ma'asumi yana nuni a kan halascin abu, amma barinsa a kan aikata wani abu ba ya nuni a kan haramcin abu. Idan muka dauka cewa sahabbai ba su yin sabo ko kuskure, wato muka yi musu hukuncin ma'asumai, a nan rashin aikatawarsu ba ya zamar mana dalili a kan haramcin abu ba. Bayan haka, ma'auni a wajen sanin haramci ko halascin abu shi ne maganar Manzo ko magadansa ma'asumai (a.s) don haka muna iya ganin wannan nau'i na Tawassuli a fili a cikin ruwayoyin Manzo da addu'o'in Ahlul baiti (a.s) Kalu balanta ta biyu: Halittu ba su da hakki a kan Allah: Wannan nau'i na tawassuli kamar wani dora nauyi ne ga Allah ta yadda dole ne Allah ya bayar da wannan hakki da ya hau kansa, alhali kuwa babu wani nauyi na wani abin halitta wanda yake a kan Allah madaukaki. Amsa: Hakkin abin halitta a kan Allah muna iya kallon sa ta fuska biyu: A-Sakamakon wasu ayyukana bawa yakan iya samun wani hakki a kan Allah kamar yadda mai bin bashi yake da hakki a kan wanda yake bi bashi. Irin wannan hakki ba zamu iya tunaninsa ba a kan Allah madaukaki daga bangaren bawa, domin kuwa bawan Allah bai mallaki komai ba, ta yadda ta hanyar wannan zai samu wani hakki a kan Allah. B-Hakin da shi da kansa Allah ta hanyar wani lutfi wanda ya yi ga shi bawa, ta wannan hanyar sai bawan ya samu hakki a wajen Allah. Wato hakikanin kuwa shi ne wata falala ce wacce Allah ya yi wa bawa sakamakon haka sai ya sanya bawan yana da wani hakki a kan Allah madaukaki, ta yadda ya sanya kansa matsayin wanda ake ba shi, shi kuma bawa matsayin mai bin bashi, bayan kasantuwar cewa wannan yana iya yiwuwa a cikin Kur'ani akwai dalilai masu tabbatar mana da hakan. Wani lokaci Allah yana daukar kansa matsayin wanda ya dauki bashi daga bayinsa, shi kuwa bawa masatyin mai ba ba bashi, a kan hakane yake cewa: "Wa zai bai wa Allah rance mai kyau". Bayan wannan akwai ayoyi da yawa wadanda suke bayani a kan cewa sakamakon wata baiwa da Allah yake wa bayinsa, zasu kasance suna samun wani hakki na musamman ga Allah wanda yake ba shi da farko ba shi da karshe. A wasu wurare ga abin da yake cewa: 1-"Ya kasance hakki a kanmu mu taimaki muminai" . 2-"Alkawari ne a kan Allah kuma hakki ne a cikin Attaura da Injila" . 3-"Kuma hakki ne a kanmu mu taimaki muminai" . 4-Karbar tuba ya wajaba a kan Allah ga wadanda suke ayyuka mummuna sakamakon jahilci, sannan sai suka tuba ba tare da jinkiri ba" . Sannan a cikin hadisai da dama zamu iya ganin irin wadannan hakkoki. Don haka a nan kawai zamukawo daya daga cikin a matsayin misali kamar haka: Manzo (s.a.w) yana cewa ya wajaba ga Allah ya taimaki wanda ya yi aure domin tsoron kada ya fada a cikin haram. Kalu bale na uku: Wannan nau'in na kamun kafa ko Tawassuli kiran wanin Allah ne. Ayoyi da yawa a cikin Kur'ani mai girma sun yi bayani a kan cewa musulmi bai halatta ba ya kira ko ya roki wanin Allah, kamar yadda Allah madaukaki yake cewa: "Kada ku kira wani tare da Allah" . "Lallai wadanda kuka kira suma bayi ne kamar ku" . Daga wadannan ayoyi guda biyu muna fahimtar cewa a wajen addu'a babu wanda ya kamata a kira sai Allah madaukaki shi kadai ba wanin Allah ba, don haka kamun kafa da wani ko matsayin wani kiran wanin Allah ne. Amsa: Abin da yake mafi rashin tushen a cikin kalu balantar da ake yi dangane da kamun kafa ko Tawassuli shi ne wannan wanda aka ambata a sama, wanda kuma da wannan ne masu kin amincewa da tawassuli suke riko da shi, ta yaddacikin rashin adalci suke dora ayoyin da suka zo a kan mushrikai masu bautar gumaka a kan musulmai da manyan bayin Allah. Duk da cewa wadannan ayoyi sun sauka ne a kan mushrikai wadanda suke daukar gumakansu matsayin alloli komasu tafiyar da duniya. Ba kamar yadda musulmi ba ya dauka cewa Manzo (s.a.w) bawan Allah ne kuma mai kira zuwa ga kadaita Allah madaukaki, sakamon ana yin amfani da irin wadannan ayoyi a wajen irin haka, don haka zamu yi dan bayani a kan wadannan ayoyi kamar haka: 1-Ayoyin da suke cewa: Kada ku kira wanin Allah, wadannan ayoyi suna nufin kiran Allah da ma'anar bauta ne, ba wai da nufin kira ba kawai ga wani mutum mai matsayi koda kuwa da niyyar cewa shi kawai wani mutum ne mai tsarki, domin kuwa a matsayin sheda a ayar da ta gabata yana cewa: "Kada ku kira wani tare da Allah". Idan cikin wannan aya ana nufin kira ko roko ne kawai ba yana nufin bauta ba ne, to zai zamana ma'anar wannan aya ta sabawa umurnin Kur'ani, domin kuwa Kur'ani yana ba da umarni ga musulmi cewa su tafi wajen Manzo su neme shi da ya roka musu Allah gafara, sannan shi ma ya gafarta musu. A nan mutum yana kiran Ubangiji yayin da yake neman gafarar Allah da kansa, sannan yana kiranmanzo yayin da yake so ya gafarta masa. Saboda haka ma'nar cewa kada ku kira wani tare da Allah shi ne, kada ku hada wani atre da Allah wajen bauta. Kamar haka ne a cikin aya ta biyu ma babu bambanci, domin kuwa abin da ake nufi da "kuke kira" a cikin aya ta biyu ana nufin bauta ne, domin kuwa jimalar da ta zo a bayanta wacce kuma take haramta yin hakan tana cewa: "Domin kuwa su bayi ne kamarku". Wato kada ku bautawa wadannan gumakan na karya domin kuwa ba su da wani bambanci da ku, suma kamarku suke bayine na Allah. Saboda haka hanin da aka yi na kada a kira wani tare da Allah ko kuma a kira shi ba tare da Allah ba, ana nufin kira ne wanda yake da ma'anar bauta, wanda ya samo asali ne daga imanin mutum da cewa shi wannan abin a matsayin Allah ne, ba wai kawai kira ba tare da wannan imanin ba, domin kuwa rayuwar dan Adam baki daya ta doru a kan haka ne. Kur'ani mai girma yana cewa: "Zamu kirawo 'ya'yammu kuma ku kirawo 'ya'yanku" . Sannan a cikin wata aya ana cewa bai kamata ku kira Manzo ba kamar yadda kuke kiran sauran mutane a tsakaninku, ga abin da ayar take cewa: "Kada ku sanya kiran Manzo kamar a tsakaninku kamar yadda kuke kiran junanku" . Saboda haka kiran da ake magana a cikin wannan aya ba ana nufin kawai kira ba haka nan, ana nufin kira da sunan bauta ga Allah ko ga wani wanda mutum ya dauka cewa shi ne yake tafiyar da wasu ayyukan Ubangiji. Don haka wadannan ayoyi guda biyu da wasu misalinsu, wace alaka suke da ita dangane da rokon da muke wa Manzo a matsayinsa na bawan Allah mai matsayi, ko kuma kawai mu kira shi ba tare da nufin ibada ba. A cikin Littattafan masu inkarin kamun kafa da wani bawan Allah, sun tattaro duk ayoyin da suke magana danagane da mushrikai da suke kiran gumakansu na karya, sannan suka dora wadannan ayoyi a kan musulmai masu kamun kafa da ruhin manyan bayin Allah. Duk da cewa tare da la'akari da wasu abubuwa guda biyu sun fita daga bahsimmu kamar haka: 1-Wadannan ayoyi suna magana ne a kan mushrikai ba masu kadaita Allah ba. 2-Kasantuwar mashrikai sun yi imani da cewa wadannan gumakansu su suke tafiyar da wasu ayyukan Ubangiji (rububiyya) shi ya sanya kira ko rokon da suke wa gumakan ya zama ibada, amma musulmai sakamakon tsarkin imaninsu da kadaita Ubangiji suna girmama bayin Allah kuma suna kamun kafa ne da su sakamakon Allah ne ya ba da iko a hakan. A takaice: haramta kira da aka yi a cikin wadannan ayoyi guda biyu, ya kasance ne sakamakon suna yin hakan ne a matsayin bauta, ba wai ko wane kira ko roko ba wanda yake baya tattare da wannan siffa. Domin kuwa mu gane wannan shiri na masu inkarin Tawassuli da bayin Allah, zamu ka wo wasu daga cikin ayoyin da suke kawowa a wajen bayanai da rubuce-rubucensu, ta yadda zai bayyana yadda suka yi amfani da wadannan ayoyi suka canza wannan al'amari, ta yadda suka dora ayoyin da suka sauka a kan mushrikai a kan musulmai, ga wadannan ayoyi kamar haka: "Wadannan wadanda suke kira ba su amsa musu da komai" . "Wadannan wadanda kuke ba zasu iya taimakonku da komai ba, sannan ba zasu iya taimakon kawunansu ba" . "Wadannan wadanda kuke kira suma bayi ne kamar ku" . "Wadanda kuke kira sabanin Allah ba su mallaki koda bawon dabino ba" . "Ka ce yanzu mun kira wanin Allah wanda ba ya amfanar da mu kuma ba ya cutar da m u" . "Kada ka kira wanin Allah wanda ba ya amfanar da kai haka nan ba ya cutar da kai" Masu inkarin Tawassuli da bayin Allah a wuraren wa'azuzuwansu da rubuce-rubucensu suna kafa hujja ne da wadannan ayoyin suna dora su a kan musulmi masu kamun kafa da bayin Allah ba tare da wani dalili ba, alhali kuwa wadannan ayoyi ba su da wata alaka da tawassuli da ake yi a cikin musulunci. Masu karatu suna iya komawa zuwa ga tafsirai domin su ga dalilan saukar da wadannan ayoyi a bayyane. Wadannan ayoyi suna magana ne da masu bautar gumaka wadanda suke da imanin cewa amfani da cutarwa, daukaka da kaskantarwa duk suna hannun wadannan allolin nasu na karya, haka nan samu nasara a wajen yaki duk yana hannunsu, ta haka ne abin da suke yi ya zama bauta, domin su samu wadannan abubuwan da suke gani suna zuwa ne daga gare su. Amma musulmi masu kamun kafa da bayin Allah akidarsu kilo mita dubu ta nisanta da wannan akida batacciya, cin nasara da kariya dukkansu suna zuwa ne daga Allah. Don haka girmamawar da suke wa ma'asumai (a.s) sam ba shi da alaka da cewa sun dauka ne su alloli ne ballantana ya zama bauta, suna haka ne domin suna ganinsu bayin Allah ne masu girma da daukaka a wajen Allah. Mafi yawa cikin addu'o'immu muna cewa ne; "Ya Allah don matsayin Manzonka Muhammad da alayansa" wannan mastayi kuwa ya yake? Wannan matsayi kuwa shi ne matsayin da Allah ya ba su, sannan Kur'ani mai girma yana ambatar wasu daga cikin annabawa da wannan matsayin kamar yadda yake cewa dangane da annabi Musa (a.s) "Ya kasance yana da matsayi a wajen Allah" . Haka nan yana cewa dangane da annabi Isa (a.s) "Yana da matsayi a duniya da lahira" . Wannan shi ne matsayin da Allah da kansa ya ambata a cikin kur'ani dangane da bayinsa, wanda sakamakon haka ne suke da kusanci da matsayi a wurin Allah madaukaki. Kalu bale na hudu: Kamun kafa yana nufin neman taimako daga wanin Allah, Mutumin da yake tawassuli a lokacin da ya shiga cikin halin kaka- na-kayi, wannan yana nufin yana neman taimako daga wanin Allah, duk da yake cewa babu wani wanda za a iya neman taimako daga gare shi sai Allah, kamar yadda Kur'ani yake cewa: "Kawai gare ka muke neman taimako". Amsa: wannan kuwa yana zama matsala ne ga mutumin da yake bai san wani abu ba daga Kur'ani, domin kuwa a baya mun yi bayani a kan cewa ana iya jingina aiki guda daya zuwa ga Allah a lokaci guda a jingina shi zuwa waninsa, haka nan mun kawo wurare da dama daga cikin Kur'ani da suke bayani a kan hakan, kamar misalin daukar rai ko rubuta ayyukan bayi, sannan muka yi bayani cewa wannan ba shi da wata matsala, domin kuwa jinginawa zuwa ga Allah a matsayin komai yana zuwa daga gare shi ne kuma sai da izinisa, jingina shi kuwa ga wani bawan Allah da ma'anar ya yi wannan aiki ne karkashin ikon Ubangiji. Allah madaukai ba tare da ya nemi taimako ba daga wani wuri yake aiwatar da ayykansa, amma waninsa yana yin hakan ne tare da izinin Ubangiji, don haka aikinsa ma aikin Allah ne da wannan ma'ana. Don haka babu matsala a lokaci guda cewa babu wanda za a nemi taimako daga gare shi sai Allah kuma a nemi taimako daga waninsa, domin kuwa neman taimako daga wani bawan Allah ba yana nufin cewa neman taimako daga gare shi maimaikon Allah. Domin kuwa yana yin komai ne da izinin Ubangiji, bisa haka ne Kur'ani yake cewa a wajen Allah kawai ake neman taimako, kuma a wani wuri yake cewa mu nemi taimako daga wanin Allah, kamar yadda yake cewa: "Ku nemi taimako daga hakuri da salla, domin kuwa suna da girma a wajen masu tsoron Allah". Zulkarnaini lokacin da yake so ya gina bango domin ya kare mutane daga harin yajuju ga abin da yake cewa mutanensa: "Abin da Allah ya hore mini ya fi abin da zaku yi mini, don haka ku taimaka mini da masu karfi" Duniya musamman duniyar mutane ta kafu ne kan taimakekeniya, sun kuma kasance suna neman taimako da sunayen annabawa da manyan bayin Allah daga junansu, sannan sam ba su ganin wannan ya saba wa asalin kadaita Allah madaukaki, domin kuwa taimakon wanin Allah yana karkashin iko ne na Allah madaukaki, wanda ya bai wa mutum wannan damar. Abin mamaki a nan shi ne wadanda suke inkarin neman taimako daga wanin Allah suna ganin ana iya neman taimako daga wanin Allah a lokacin da yake raye, amma bayan ya mutu ya haramta kuma yin hakan ma shirka ne, alhalin idan abu shirka ne kasantuwar bangare guda yana da rai da bashi da rai ba ya canza wannan abu, saboda haka neman taimako daga wani idan har ya kasance muna ganin cewa yana iya yin hakan ne tare taimakon Allah sam ba shirka ba ne, wannan kuwa ya kasance yana da rai ne ko kuwa bayan mutuwarsa ne. Daga karshe zamu yi tunatarwa a kan wasu abubuwa guda uku kamar haka: 1-Ruwayoyin Halascin Tawassuli Ko Kamun kafa, Mutawatir Ne Ruwayoyi da suke magana a kan Tawassuli wadanda muka kawo kadan daga Littattafan AhlusSunna kodai mutawatir ne ko kuma gab suke da su zama mutawatir, saboda haka ba zai yiwu ba ta hanyar raunana danganen wadannan ruwayoyi mu yi inkarin wannan al'amari, domin kuwa wadannan ruwayoyi suna nuni da cewa wannan al'amari ya kasance kamar ruwan dare a tsakanin al'ummar musulmi a tsawon tarihi, idan har mun kauce wa ambatar wasu da hakacikin wadannan ruwayoyi da suke magana a kan Tawassuli wadanda wasu daga cikinsu ta fuskar sanad ko dangane suna da rauni, wannan ba zai cutar da abin da muke managa a kansa ba, kamar yadda muka san cewa al'amarin haka yake dangane da hadisi mutawatir. 2-Littattafai Dangane Da Tawassuli Al'amarin Tawassuli ko kamun kafa da bayin Allah, wani abu ne wanda yake an sallama a kansa a cikin musulunci, sakamkon haka ne manyan malaman hadisi da na fikihu sun rubuta littafai da dama a kan wannan mas'ala tun kafin Ibn Taimiyya da kuma bayansa, wadanda a nan kawai zamu kawo wasu daga cikinsu: 1-Alwafa fi fadha'ilul Mustafa Ibn jauzi (Ya rasu shekara ta 597) a cikin wannan littafi akwai babi na musamman wanda yake magana a kan kamun kafa da Manzo da neman ceto da shi da kabarinsa mai albarka. 2-Misbahuz zulam fi mutagisina bi khairi anam, wanda ya rubuta shi Muhammad Bn Nu'uman Maliki (ya rasu shekara ta 973) Samhudi a cikin littafinsa wafa'ul wafa ya ruwaito da dama daga wannan littafi dangane da Tawassuli. 3-Al-bayan wal ikhtisar, wanda Ibn Daud Maliki shazali ya rubuta, a cikin wannan littafi ya kawo yadda manyan malamai da bayin Allah suke kamun kafa da Manzo (s.a.w) 4-Shifa'us sikam, wanda Takiyyuddin Subki ya rubuta ya yi kariya da kyau a kan kamun kafa da Manzo a cikin wannan littafi nasa. 5-Wafa'ul wafa li'akhabari daril Mustafa, wanda Sayyid Nuruddin samhudi ya rubuta, (ya rasu shekara ta 911) ya yi Bahasi a kan Tawassuli a cikin juz'i na hudu na wannan littafi. 6-Al-mawahibud daniyya wanda Abu Abbas kustalani (ya rasu a shekara 933) ya yi bahsin Tawassuli a cikin wannan littafi nasa. 7-Sharhul mawahibud diniyya, wanda Misri zarkani ya rubuta, (ya rasu a shekara ta 1122) ya yimaganar Tawassuli a cikin mujalladi na takwas. 8-Sulhul Ikhwan: Wanda Khalidi Bagdadi ya rubuta, (ya rasu a shekara ta 1299) a cikin wannan littafi ya rubuta risala ta musamman raddi a kan Alusi bayan rasuwarsa a shekara ta 1306 a ka buga littafin. 9-Kanzul matalib: wanda Adwi Ahmzawi ya rubuta, (ya rasu shekara ta1303). 10-Furkanul kur'an wanda Izami shafi'i ya rbuta. Amma ta bangaren Shi'a an rubuta littafai masu yawa a kan haka, a nan kawai zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka: 1-Sabilur rashad liman aradas sadad, wanda sheikh Ja'afar Kashiful Gida ya rubuta, (ya rasu 1227) an buga wannan littafi saudayawa. 2-Kashful irtiyab, wanda Sayyid Jabalil Amuli ya rubuta, (1282-1373). 3-Al-gadir, Allama Amini ya yi Bahasi mai tsawo a kan wannan magana. 3-Sabani Tsakanin Mabiya Ibn Taimiyya Da Sauran Musulmi An rubuta wasu litattafai daga bangaren masu inkarin tawassuli da bayin Allah daga bayan-bayan nan, inda suke nuna cewa wani sabani ne tsakanin Shi'a da Sunna, alhalin kuwa wannan sabani bai shafi tsakanin Sunna da Shi'a ba, wani sabani ne wanda yake tsakanin mabiya Ibn Taimiyya da sauran al'ummar musulmi, kuma a baya kadan mun kawo wasu Littattafan manyan malaman AhlusSunna wadanda aka rubuta a kan raddi ga Ibn Taimiyya da mabiyinsa Muhammad Bn Abdul wahab, don haka muna iya gane cewa sabani ya fari ne tsakanin wadannan mutum biyu da mabiyansu da sauran dukkan al'ummar musulmi wadanda suka tafi a kan ingancin kamun kafa da waliyyan Allah, wato sauran musulmi ba su da sabani a kan haka, don haka ba sabani ne ba tsakanin Shi'a da Sunna kamar yadda wasu suke riyawa, kamar yadda muka gani da kuma abin da zamu gani a nan gaba wanda yake tabbatar da hakan. Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP) Facebook: Haidar Center - December, 2012