Tawassuli (Kamun Kafa)2
  • Take: Tawassuli (Kamun Kafa)2
  • marubucin: Sheikh Subhani
  • Source:
  • Ranar Saki: 3:38:58 4-9-1403

Tawassuli (Kamun Kafa)2

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI


Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2

Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Yanzu kuma lokaci ya yi inda zamu bayyanar da kashe-kashen neman tsani ko kamun kafa da wata ma'anar, sannan mu yi bayanin hukuncin kowane ta yadda ya dace da Kur'ani da Sunna ko kuma sabanin hakan.
Kamun kafa yana da kashe-kashe kamar yadda zamu ambata a kasa kamar haka:
1-Kamun kafa Da Sunaye Da Siffofin Allah
Daya daga cikin rabe-raben kamun kafa ko neman tsani zuwa ga Allah shi ne neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar kiran sunaye da siffofinsa. Wannan nau'i kuwa na kamun kafa ko tawassuli ya zo da yawa a cikin ruwayoyin Ahlul baiti (a.s), amma a nan kawai zamu wadatu da hadisai guda biyu da suke nuni a kan haka:
Tirmizi a cikin Sunan dinsa ya ruwaito daga Buraida shi kuma daga Manzo (s.a.w) cewa yaji wani mutum yana cewa: Ya Allah ina rokon da kasantuwar na sheda cewa babu abin bauta da gaskiya sai kai, sannan kai kadai ne kuma mai biyan bukata, sannan ba a haife ka ba kuma ba ka haifa ba, sannan babu wani wanda ya yi daidai da kai.
Sai Manzo ya ce masa lallai ka roki Allah da babban suna wanda idan aka kira sa da shi zai amsa, idan kuwa aka roke shi da shi zai bai wa mutum abin da ya nema.
2-Ya zo a cikin wata addu'a Imam Bakir da Imam Sadik (a.s) suna cewa: "Ya Allah ina rokon ka da babban sunanka wanda ya fi kowane girma, mafigirma da daukaka wanda idan aka roke ka da shi domin kofofin da suke a kulle a sama ana so su bude zasu bude, sannan idan aka kira ka da shi domin fadada kofofin da suke kasa zasu fadada, kuma idan aka roke ka da shi domin samun sauki, za a samu saukin. "
2-Kamun kafa Da Kur'ani
Daya daga cikin hanyoyin da ake kamun kafa da su domin neman kusanci ga Ubangiji shi ne mutum ya karanta Kur'ani, ta wannan hanyar sai Allah ya biya masa bukatarsa. A hakikanin gaskiya wannan nau'in kamun kafa, kamun kafa ne da ayyukan Ubangiji, domin kuwa Kur'ani maganar Allah ce wacce ta sauka a kan zuciyar Manzo (s.a.w)
Ahmad Bn Hambal ya ruwaito daga Imran Bn Husaini yana cewa: Na ji daga manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Ku karanta Kur'ani ku roki Allah da shi, kafin wasu gungun mutane su zo wadanda zasu roki mutane da shi.
Idan muka lura da kyau a cikin wannan hadisi yana nuna mana wani abu, wannan kuwa shi ne, kamun kafa da duk wanda yake da girma da matsayi a wajen Allah wani abu ne wanda ya halatta, saboda mustahabbi ne a daren lailatul kadari mutum ya buda Kur'ani ya karanta ya roki Allah da shi tare da wannan addu'a kamar haka: "Ya Allah ina rokonka da wannan Kur'ani da abin da ka saukar a cikinsa, a cikinsa akwai babban sunanka da sunayenka kyawawa…
3-Kamun kafa Da Kyawawan Ayyuka
Kamar yadda muka ambata a farkon wannan Bahasi cewa idab mutum yana so ya cimma wani abu na rayuwar duniya ta hanyar hankalinsa ne zai gano ta wace hanya ce ya kamata ya bi domin ya cimma wannan abin da yake nema. Wato mutum ya san abin da ya dace ya aikata domin ya biya bukatunsa na rayuwa, misali kamar idan mutum yana jin yunwa ko kishirwa ya san cewa abinci ko ruwa zai sha don ya yi maganin wannan kishirwa da yunwar. Amma dangane da abin da ya shafi ruhi ko lahira, ba zai yiwu ba mutum ya iya gano hanyar da zai bi don ya cimma abin da yake so ya cimmawa, saboda haka a nan yana da bukatuwa zuwa Allah ko wakilinsa wanda zai gwada masa hanyar da ya kamata ya bi, sannan ba tare da jagorancinsa ba babu yadda zai yi ya isa zuwa ga hadafinsa, domin kuwa bin wata hanya wacce ba shari'a ba ce ta bayyana hakan zai zama bidi'a a cikin addini. Saboda haka musulmi dole ne a nan dangane da abin da ya shafi addini ya yi riko da abin da yazo a cikin Kur'ani da Sunna.
Kamun kafa da kyawawa kyawawa wanda shi ne nau'i na uku a cikin wannan Bahasi, a cikin Kur'ani an yi nuni da shi duk da cewa ba a bayyane ba ne kamar yadda ya zo a bayyana ne a cikin hadisai, bayaninsa kuwa atakaice shi ne, idan mutum ya aikata wani aiki domin Allah, yayin da mutum ya shiga wata matsala, yana iya ambatar wannan aikin da ya yi mai kyau domin Allah madaukaki ya yaye masa matsalar da ya shiga. Kai duk lokacin da mutum ya aikata wani aiki mai kyau yana iya rokon Allah da ya biya masa bukata da wannan aiki da ya aikata. Ga wasu abubuwa da suka zo a tarihi wadanda suke ba da sheda a kan hakan.
1-Annabi Ibrahim yayin da yake gina dakin ka'aba, ya roki Allah da ya sanya shi da dansa Isma'il su kasance masu biyayya ga Allah. Ga abin da Kur'ani yake cewa a kan haka: "A lokacin da Ibarahim shi da Isma'il suke daga ginin Ka'aba, sai suka ce ya Allah ka karba mana kai ne mai ji masani. Ya Allah ka sanya mu masu mika wuya gare ka, sannan daga zuriyar mu ka sanya su masu mika wuya a gareka, ya Allah ka koyar da mu ayyukan hajji, ka kuma karbi tubarmu, lallai kaine mai karbar tuba mai jin kai. " Mun ga yadda annabi Ibarahim da dansa Isma'il suka yi kyakkyawan aiki na ginin dakin ka'aba, a wannan lokaci sai suka roki Allah wasu abubuwa kamar haka:
A-Karbar wannan aiki daga dukkan su biyun.
B-Allah ya sanya su masu biyayya a gare shi.
C-Koyar da su aikin hajji.
D-Karbar tubarsu da sanya su a cikin rahama.
2-A cikin wata ayar ga abin da ya zo: "Muminai wadanda suke cewa: Ya Allah lallai mun yi imani ka yi mana gafara a kan zunubbammu, sannan ka tseratar da mu daga azabar wuta".
A cikin wannan aya sun roki Allah da cewa ya gafarta musu zunubbansu sakamakon ayyukan kyawawa inda suke cewa "lallai mun yi imani da kai".
Kamar yadda muka yi bayani a baya, ayoyin Kur'ani sun yi nuni da halascin kamun kafa da ayyuka na gari duk da cewa ba a bayyane ba ne. Amma a cikin ruwayoyi an yi bayanin hakan a fili. Sannan masu ruwaito hadisi daga bangarori guda biyu, sun ruwaito cewa wasu muminai guda uku sun kasance a cikin daji, sai ruwan sama ya taso, sai suka shiga cikin wani kogo domin su buya. Amma cikin rashin sa'a sakamakon wannan ruwa da iska sai wani bangaren dutse ya gangaro daga sama ya rufe kofar wannan kogo, a wannan lokaci sai daya daga cikinsu ya ce: Fadin gaskiya ce kawai abin da zai fitar da mu daga cikin wannan dutse, don haka ku zo duk wanda ya yi wani kyakkyawan aiki ya fada, sai mu roki Allah sakamakon albarkacin wannan aiki ya tseratar da mu. Dukkansu ukun suka fadi wani aiki wanda suka yi saboda Allah, kamun kafar da suka yi da wadannan ayyuka na su, cikin ikon Allah sai wannan dutse ya bude suka fita daga wannan hali da suka shiga.
Malamin Hadisi Baraki (ya rasu shekra ta 274) bayan ya ambaci wannan labari sai ya ce: Daya daga cikinsu cewa ya yi, ya kasance na baiwa wata mace kudi domin mu aikata wani aiki wanda bai dace ba, sannan kuma ita ma ta shirya a kan hakan, amma sai na tuna cewa akwai azabar lahira ga masu yin hakan, sai na kaurace wa wannan aiki, a wannan lokaci sai kofar ta dan bude kadan.
Sai daya kuma daga cikinsu shi ma ya ce:
Na ksance na tara wasu mutane domin su yi mini aikin kwadago, sannan zan ba kowane daya daga cikinsu rabin darhami matsayin ladar aikinsu. Bayan sun gama wannan aiki sai wani daga cikinsu ya nemi in ba shi darhami guda, wato a matsayin shi ya yi aikin mutum biyu ne, amma sai ban amince da abin da ya fada ba, sai bai amshi komai ba ya fita, (sai na kasance na yi amfani da kudin na wadanda suke a hannuna) na yi noma sannan kuma na samu amfani mai yawa. lokacin da ya ji wannan labari sai ya zo a wajena, sai ba shi darhami dubu goma, ya Allah na yi wannan aiki ne domin neman yardarka. a wannan lokaci sai kofar kogo ta dan kara budewa.
Sai na ukkunsu ya ce: Wata rana na kawo wa babana da mamana kwanon madara sai na tarar da su duk suna barci. Sai na yi tunani a cikin raina cewa idan na ajiye musu wannan madara a kasa na tafi gida mai yiwuwa kafin su tashi kuda ko sauro ya fada musu a cikin wannan madara, sannan kuma ba ni so in tayar da su daga barci. saboda haka sai na yi tsaye da wannan madara har suka ta shi daga barci sannan suka sha wannan madara. A wannan lokaci sai kofar kogo ta bude dukkanta suka fita daga wannan hali da suka shiga.
Wannan kissa kuwa masu hadisi daga bangare guda biyu Sunna da Shi'a sun kawo ta duk da cewa akwai sabani a wasu abubuwa.
4-Kamun kafa Da Adu'ar Manzo (s.a.w)
Manzo (s.a.w) mutum ne wanda yake ya fi kowa girma da daukaka a cikin dukkan halittar da Allah ya yi, Ayoyin Kur'ani sun yi nuni da haka a wurare da dama, saboda haka ba zai yiwu ba mu kawo dukkansu a wannan wuri.
Dangane da darajar Manzo ya wadatar da mu a kan cewa yana matsayin mai kare al'umma daga azabar Allah, Allah yana bayyanarwa a cikin Kur'ani cewa, matukar Manzo yana a cikin al'umma to Allah ba zai kama wannan al'ummar ba da azaba ba, kamar yadda yake cewa: Allah bai kasance zai azabtar da su ba matukar kanacikinsu, sannan Allah ba zai azabtar da sub a matukar suna neman gafara".
Sannan ya wadatar da mu a kan girman Manzo inda Allah madaukaki ya sanya sunan Manzo a gefen sunansa, sannan ya sanya biyayya ga Manzo tare da biyayya ga Allah, a kan haka Allah yana cewe: "Duk wanda ya bi Allah ya bi Manzo, lallai ya samu babban rabo".
Wadannan ayoyi da masu kama da su suna bayyanar da dajara da karama ta Manzo (s.a.w) matsayi da darajar da babu wani a cikin halitta wanda yake da shi, sakamakon wannan matsayin da daukaka da Manzo yake da shi a wajen Allah duk abin da yaroka za a biya masa bukatarsa. Don haka ne aka bai wa masu laifuka da zunubbai umurnin cewa, su nemi Manzo daya nema musu gafara a wajen Allah, inda Allah madaukaki yake cewa: "Da wadanda suka zalunci kawunansu zasu zo maka suna masu neman gafara a wajen Allah, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai gafara kuma mai karbar tuba".
Sannan zamu iya fahimta daga wasu ayoyi cewa, sakamakon matsayi da daukaka manzanni sun kasance ana iya kamun kafa da su a wajen Allah kamar yadda zamu gani dangane da 'ya'yan annabi Yakub (a.s) lokacin da kuskuransu ya bayyana a fili, sai suka cewa mahaifinsu: "Ya babanmu ka nema mana gafara lallai mun kasance masu kuskure. Sai ya ce musu zan nema muku gafara a wajen ubangijina, kuma lallai shi mai gafara ne mai rahama".
Dangane da halascin wannan nau'i na kamun kafa babu wani shakku a cikinsa, domin kuwa babu sabani a kan haka. Abin da yake da muhimmanci a nan shi ne, sanin dalilin da ya sa nya ake karbar addu'ar annabawa.
Babu shakka tushen abin da ya sanya ake karbar addu'ar annabi ya samo asali ne daga tsarkin ruhinsa, sannan da kusancinsa ga Allah madaukaki. Don haka sakamakon wannan girma da daukaka ne na ruhi ya sanya Allah yake karbar addu'arsu.
Babu shakka addu'ar da ta taso daga ruhi mai tsarki wanda yake cike da soyayyar Ubangiji, ba tare da wani bata lokaci ba zata samu karbuwa a wajen Allah madaukaki.
Idan har akwai wata magana a kan halascin wannan kamun kafa kuwa, zai kasance ne dangane da kamun kafa da annabawa yayin da suka rasu wato lokacin da ba su raye a duniya. Tare da kula da abin da muka fada a wajen ziyarar kabari, mun yi bayani kan cewa babu wani bambanci tsakanin lokacin da annabawa suke a raye da lokacin da ba su raye a duniya, domin kuwa Manzo a cikin wadannan hali guda biyu yana iya nema wa mutum gafara a wajen Allah. Zamu yi cikakken bayani a kan wannan a cikin nau'in kamun kafa na shida insha Allah.
5-Kamun kafa Da Addu'ar Dan'uwa Mumini
Kur'ani yana bayyanar da cewa mala'iku suna yi wa masu imani addu'a, kamar haka:
"Wadanda suke daukar al'arshi da na gefensa, suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, kuma suna masu imani da shi, sannan suna neman gafara ga wadanda suka yi imani" .
Wannan ba yana nuna cewa ba mala'iku ne kawai suke yi wa masu imani addu'a. Domin kuwa Kur'ani a fifli yana bayar da labarin yadda muminai suke wa junansu addu'ga abin da Kur'ani yake cewa: "Wadanda suka zo a bayansu, suna cewa, ya ubangijinmu! Ka yi mana gafara da 'yan'uwammu wadanda suka riga mu da imani, ya Allah kada ka sanya jin zafin a cikin zukatanmu dangane da wadanda suka yi imani, ya Allah kai ne mai rangwame mai rahama".
A cikin ayoyin da muka ambata a sama zamu iya fahimtar cewa, addu'ar mala'iku masu daukar al'arshi da kuma addu'ar muminai a kan 'yan'uwansu ta cancanci karbuwa. Saboda haka wannan aya tana nuna mana cewa mutum yana iya neman addu'a daga mala'ku da kuma sauran 'yan'uwansa masu imani.
Dangane da karbar adduar mumini kuwa, ya wadatar da mu inda Manzo (s.a.w) yake neman muminai su yi masa addu'a, inda yake cewa: Ku nema mini tsani a wajen Allah domin kuwa matsayi ne a cikin aljanna, babu kuwa wanda zai samu wannan matsayin sai wasu da suka cancanta daga cikin bayinsa, ina fata in zama nine, don haka duk wanda ya nemi kamun kafa da ni, cetona ya halasta gare shi". Kasantuwar wannan kamun kafar ya karbu a wajen dukkan musulmi ba tare da wani sabani ba, muna iya wadatuwa da wannan.
6-Kamun kafa Da Addu'ar Manzo Bayan Rasuwarsa
Bahsin da ya gabata ya tabbatar mana yadda kofofin rahama suka kasance a bude ga masu laifuka, ta yadda zasu iya kamun kafa da Manzo kamar yadda aya take nuni da hakan (da wadanda suka zalunci kawunansu sun…) wato suka nemi Manzo da ya neman musu gafara a wajen Allah. Sakamakon haka ne Kur'ani yake zargin munafukai domin kasantuwarsu sun rasa wannan falalar mai dimbin yawa. Ga abin da yake cewa: "Duk lokacin da aka ce musu, ku tafi zuwa Manzo domin ya nema muku gafara sai su kawar da kansu".
A nan akwai abin tambaya: shin sakamakon tafiyar Manzo zuwa ga rahamar Ubangiji wannan kofar gafarar da jin kai shi kenan ta kulle, ta yadda babu wani musulmi da zai je wajen Manzo ya roke shi da ya nema masa gafara a wajen Allah, ko kuwa wannan kofar albarka tananan bude kamar lokacin da yana raye? Wato musulmi har yanzu idan suka je haraminsa suna iya neman addu'arsa, ta yadda wannan ayar da muka ambata; "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka neme ka da nema musu gafarar..". tana amfani a dukkan lokuta guda biyu, wato zamanin raywarsa da kuma bayan wafatinsa?
A wajen bayar da wannan masa dole ne a ce: Musulmi daga sahabbai da tabi'ai har zuwa yanzu sun kasance a aikace suna daukar wannan kofa a bude take, sannan musulmai a lokacin da suka ziyarci raudhar Manzo bayan yi wa manzon tsira sallama sukan karanta wannan ayar da muka ambata, tare da neman gafara daga Allah kuma suna rokon Manzo da ya nema musu gafara a wajen Allah madaukaki, saboda haka duk lokacin da mutum ya je ziyarar Manzo zai ga wannan al'amari daga al'ummar musulmi.
Bayan abin da tarihi yake nunawa ta hanyar ayyukan al'ummar musulmi danagane da neman addu'ar Manzo, addu'ar ziyarar Manzo ma wacce sunna da Shi'a suka ruwaito wannan addu'a tana tabbatar da wannan magana ta neman addu'ar Manzo. Domin jan hankalin masu karatu kuma suka kara natsuwa da abin da muke magana a kai, zamu kawo wassu daga cikin maganganunsu, ta yadda zai bayyanar mana yadda manyan malamai tun tsawon zamani suke neman kamun kafa da Manzo wajen yi musu addu'a:

1-Zakariya Muhyiddin Nawawi (631-676) Yana rubuta cewa: Mai ziyara yakan fuskanci Manzo ya yi kamun kafa da Manzo a kan abin da yake bukata kuma ta hanyarsa ya nemi ceto daga Allah, yana daga abu mafi kyau kasantuwar Mawardi, Alkali Abu Tayyib da wasu daga cikin manyan malamai suka ruwaito daga Utba tare da yabo suna cewa:
Utba yana cewa: Na kasance a wajen Manzo (s.a.w) wani mutum daga daji ya zo wajen Manzo ya ce "Assalamu alaika ya rasulullah, na ji Allah yana cewa: "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka nemi gafara, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai"Lallai na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina sannan mai neman ceto a wajen Allah tare da kamun kafa da kai".
Kada mu yi tunanin cewa Nawawi ne kawai da malamansa suka tafi a kan ingancin kamun kafa da neman ceto daga Manzo. Malaman fikhu da na hadisi da dama sun kawo wannan a cikin littafansu na ziyara.
2-Kuddama Hambali (ya rasu shekara ta 620) a cikin ladubban ziyarar kabarin Manzo inda yake kawo maganar cewa"Mustahabbi ne ziyarar Manzo" Yaruwaito daga Abu Huraira yana cewa Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya yi mini sallama, zan amsa masa sallamarsa. Sannan sai ya ruwaito daga Utba abin da muka ambata a baya kadan cikin hadisin Nawawi. Ya ce manufarsa wajen kawo wannan hadisi shi ne, don ya nuna cewa ana gabatar da ziyarar Manzo kamar haka:
3-Samhudi a cikin littafin "Mustau'ab" wanda Muhammad Bn Abdullah Samiri Hambali ya rubuta, yana ruwaito yadda ake ziyarar Manzo kamar haka:
Assalamu Alaika ya Rasulallah, assalamu alaika ya Nabiyyallah! Ya Allah kai ne ka fada a cikin littafinka ga annabinka cewa: "Da wadanda suka zalunci kawunansu…Ya Allah ga ni na zo wajen manzonka (s.a.w) ina mai neman gafara, ya Allah ina rokonka a kan ka wajabta mini rahamarka, kamar yadda ka wajabta ga wanda ya zo wajensa yayin da yake a raye, ya Allah ina ina kamun kafa da annabinka zuwa gare ka".
4- Gazali (ya rasu 505) Dangane da falalar ziyarar Madina da yadda ake ziyarar Manzo ya ruwaito a bayyane yana cewa: Bayan mutum ya gama sallama ga Manzo, sai ya dubi kabarin Manzo yana tsaye, sannan ya yi godiya ga Allah da yabonsa, sai ya aika gaisuwa mai yawa zuwa ga Manzo, sannan ya karanta wannna ayar da take cewa: Da wadanda suka zalunci kawunansu sun zo, sannan ya ce ya Allah mun ji kiran ka kuma mun amsa umurninka, sannan mun yi kamun kafa da manzonka muna neman cetonka daga zunubbammu, lallai zunubbai masu nauyi sun yi mana yawa…"
5- Sheikh Hasan Bn Ammar sharanbalani a cikin littafinsa "Murakil falah" yana ruwaito ziyarar Manzo kamar haka:
"Amincin Allah ya tabbata gareka ya kai shugabana ya manzon Allah, Amincin Allah ya tabbata a gareka ya annabin Allah! Lallai kurakurai sun karya mana kashin baya, sannan nauyin zunubban ya yi mana yawa a kan kafadummu. Kai ne mai ceto kuma wanda ake karbar cetonsa. Allah madaukaki ya yi maka alkawarin ceto da matsayi mai girma kuma abin yabo a wurinsa, sannan yana cewa: "Duk lokacin da suka zalunci kawunansu sannan suka zo wajenka suna masu neman gafarar Allah sannan Manzo ya nema musu gafara a wajen Allah, zamu samu Allah mai karbar tuba kuma mai jin kai.
Mun kasance mun zalunci kawunammu ga mu mun zo wajenka sannan muna neman gafara dangane da zunubbammu, ka nema mana gafara a wajen Allah".
6- Sayyid Ibn Dawus (ya rasu 664) ya ruwaito yadda ake ziyarar Manzo daga Imam Sadik (a.s) ga abin da yake cewa: Ya Ubangiji kai ne ka ce wa manzonka duk lokacin da suka zalunci kawunansu kuma suka zo wajenka suna neman gafarar Allah, sannan Manzo yanema musu gafara, zasu samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai"
Ya Ubangiji ban kasance ina rayuwa a zamanin Manzo ba, amma yanzu na zo ziyararsa, kuma ina mai tuba daga munanan ayyukana, kuma ina neman gafara daga zunubbaina kuma ina mai ikrari a kan aikata su".
Mun kawo wasu daga cikin misalai dangane da yadda ake ziyarar Manzo, sannan mun ga yadda suka hadu a kan karanta wannan aya ga mai ziyara. A hakikanin gaskiya wannan aya wani nauyi ne aka aza wa mai ziyara aka kuma aza wa Manzo:
Amma nauyin da aka aza wa mai ziyara shi ne, mutum ya je wajen Manzo ya nemi gafarar zubbansa, sannan nauyin da ya hau kan Manzo shi ne ya neman wa mai ziyara gafara a wajen Allah.
Dukkan wadannan ladubban ziyara suna nuna mana yadda mai ziyara yake neman ceto daga Manzo a yayin da ba shi duniya, babu bambanci da lokacin da yake raye ta yadda mutum zai yi kamun kafa da shi.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012