Ziyarar Kabari2
  • Take: Ziyarar Kabari2
  • marubucin: Sheikh Subhani
  • Source:
  • Ranar Saki: 22:4:17 1-10-1403

Ziyarar Kabari2

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI


Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma A Mahangar Malaman Hadisi Da Fikihu
Tare da bibiyar maganganun manyan malaman hadisi da malaman fikihu, zamu ga yadda kodayauhse malaman musulunci suke karfafawa a kan kasantuwar ziyarar kabarin Manzo a matsayin mustahbbi mai karfi, Sannan suna kiran mutane zuwa ga ziyarar kabarin Manzo mai tsarki.
Takiyyuddin Subki Shafi'i (ya rasu shekara ta 756) Wanda yake daya daga cikin manyan malaman karni na takwas. Yayin da yake kalu balantar akidun Ibn Taimiyya wanda yake inkarin ziyarar kabarin Manzo (s.a.w), ya rubuta littafi mai suna (shifa'us sikam fi ziyarati khairil anam) a cikin wannan littafi ya yi kokari ya tattaro ra'ayoyin malaman AhlusSunna tun daga karni na hudu har zuwa lokacinsa a kan wannan al'amari, a cikin wannan littafi nasa ya yi kokarin tabbatar da nuna cewa ziyarar kabarin Manzo yana daga cikin abubuwan da aka sallama a cikin fikihu a kan cewa mustahabbi ne. Manyan malaman hadisi da fikhu sun ruwaito hadisai daban-daban a kan kasantuwar ziyar Manzo a matsayin mustahabbi, sannan suka ba da fatawa a kan hakan.
Allama Amini wanda yake bincike na wannan zamani kuma mai tsanantawa wajen bincikensa (1320-1390), a cikin babban littafin nan nasa "Algadir" Ya yi kokari wajen cike abin da ya ragu a kan wannan magana ta ziyar kabarin Manzo, inda ya yi kokari ya zo da ra'ayoyin malamai arbai'n wadanda suka hada da malaman hadisi da na fikhu har zuwa malaman zamaninsa.
Wannan marubuci shi ma ya yi kokari ya samo wasu daga fatwoyin da ba su zo ba a cikin wadancan Littattafan guda biyu da muka ambata. Ta yadda ya kawo su a cikin wani karamin littafi da ya rubuta a cikin harshen larabci.
Kai har da babban mai fatawar Kasar Sa'udiyya wato sheikh Abdul Aziz Bn Baz ya ba da fatwa a kan mustahabancin ziyarar kabarin Manzo mai girma.
Kawo dukkan maganganun malamai a kan wannan al'amari, ba zai yiwu ba a wannan wuri, saboda haka kawai zamu wadatu da kawo wasu daga ciki ne kawai kamar haka:
1-Abu Abdullaji Jujani Shafi'i (ya rasu a shekara ta 403) Bayan ya yi maganganu a kan girmama Manzo sai yake cewa: A matsayin tuanatarwa a yau ziyarar Manzo shi ne ziyarar kabarinsa mai albarka.
2-Abu Hasan mawardi (ya rasu a shekara ta 450) Yana rubuta cewa: Jaogoran matafiya zuwa aikin hajji bayan an gama aikin hajji sai ya jagoranci twagarsa zuwa madina domin mahajjata su hada ziyara guda biyu, wato ziyarar dakin ka'aba da ziyarar kabarin Manzo. Ta haka ne zasu kiyaye martabar Manzo suka kuma bayar da hakkinsa na biyayya gare shi. Ziyarar kabarin Manzo ba ya daga cikin farillan ayyukan hajji, amma yana daga cikin mustahabban aikin hajji.
3-Gazali ya yi bayani mai fadi dangane da ziyar Manzo (s.a.w). Sannan ya yi bayani a kan ladubban ziyarar Manzo Yana cewa: Manzo ya ce: ziyarata yayin da ba ni da rai duk daya ne da ziyarata a lokacin da nake raye. Sannan duk wanda yake da karfin jiki da dukiya amma bai ziyarce ni ba to ya yi mani tozarci.
Gazali yana karawa da cewa: Duk wanda ya yi nufin ziyarar Manzo to ya aika masa da gaisuwa a bisa hanya, sannan a lokacin da idonsa ya hangi itatuwa da bangayenmadina sai ya ce: Ya Allah wannan shi ne haramin Manzonka ka sanya shi kariya a gareni daga wuta, Sannan ya zama aminci a gare ni daga azabar wuta da munin hisabi.
Sannan gazali ya yi tunatarwa dangane da ladubban ziyarar Manzo yana rubuta cewa: Wanda ya ziyar Manzo sai wuce a "Bakiyya"don ya ziyarci kabarin Imam Hasan Bn Ali (a.s) Sannan ya yi salla a masallacin Fadima (a.s).
4-Alkali Iyadh maliki (ya rasu a shekara ta 544) yana rubuta cewa: Ziyara Manzo wata Sunna ce wadda kowa ya aminta da ita.
Sannan ya ruwaito wasu hadisai dangane da ziyarar kabarin Manzo sannan yana karawa da cewa: maziyarcin kabarin Manzo, to ya kamata ya nemi tabaraki da wurin ibadar Manzo (Raudha) Minbarinsa, wurin da yake tsayawa, da shika-shikan da Manzo yake jingina a wurinsu da kuma wurin da jibra'il yake saukar wa Manzo da wahayi.
5-Ibn Hajjaj Muhammad Bn Abdali Kirawani Maliki (ya rasu a shekara ta 738) bayan ya yi Magana dangane da ziyarar manzanni da ladubbanta da yadda ake yin kamun kafa (tawassuli) da su da neman biyan bukata daga garesu, sai ya tunatar dangane da ziyarar kamar haka:
"Abin da muka fada dangane da wadansu, a kan abin da ya shafi ziyarar shugaban wadanda suka gabata da wadanda zasu zo kuwa da yadda ake yi masa salla dole ne mu fadi abin da ya wuce hakan. Abin da ya dace shi ne mutum tare da kaskantar da kai ya halarci haramin Manzo domin kuwa shi mai ceto wanda ba a mayar da cetonsa. Duk wanda ya tunkare shi ba zai koma ba yana mai yanke kauna ba. Sannan duk wanda ya zo haraminsa yana neman taimakonsa da biyan buakatarsa ba zai rasa abin da yake nema ba. "
Sannan ya cigaba da cewa: Malamammu (Allah ya gafarta musu) Suna cewa abin ya dace shi ne, wanda ya ziyarci Manzo ya rika jin cewa kamar Manzo yana raye ne ya ziyarce shi. "
6-Ibn Hajar Haitami Makki Shafi'i (ya rasu shekara ta 973) Ya kasance ya yi riko da dalilin da dukkan malamai suka hadu a kansu wajen kafa hujja a kan kasantuwar mustahabbancin ziyarar Manzo. Sannan yana karawa da cewa: Sabawar wani malami guda a kan wandannan dalilai kamar Ibn Taimiyya ba ya cutar da wadannan dalilai da a ka hadu a kan ingancinsu. Domin kuwa malamai da yawa sun bibiyi maganganusa kuma suna rashin ingancinsu. Daya daga cikinsu kuwa shi ne Izz Bn Jama'a ne. Kamar yadda Ibn Hajar yake cewa: "Ibn Taimiyya mutum ne wanda Allah ya batar da shi, Sannan ya sanya masa tufafin kaskanci". Sannan Sheikh Takiyyuddin Subki wanda dangane da matsayinsa na ilimi kowa ya aminta da shi, littafi na musamman ya rubuta don kalu balantar fatwowiyin Ibn Taimiyya.
7-Muhammad Bn Abdul wahab yana cewa: Mustahabbi ne ziyayar Manzo amma wajibi ne mutum ya yi tafiya zuwa wajen domin ziyara da yin salla a wajen.
8-Abdurrahman Jaziri marubucin littafin nan (Alfikhu Ala Mazahibil Arba'a) Inda kawo fatwowiyin dukkan malaman mazahaba guda hudu na Sunna, yana cewa: Ziyarar kabarin Manzo yana daya daga cikin manyan mustahabbai, sannan hadisai sun zo a kan hakan, sannan ya cigaba da kawo hadisai guda shida da suka yi bayanin a kan ziyarar Manzo da ladubbanta.
Sakamakon cewa duk shugabannin fikhu guda hudu ba su yi wani Karin bayani ba akan abin da aka ambata a sama ba, yana nuna cewa duk malaman wannan zamani suma sun tafi a kan hakan.
9-Shekh Abdul Aziz Bn Baz yana cewa: Duk wanda ya ziyarci Manzo mustahabbi ne ya yi salla raka'a biyu a (radahar Manzo) Sanna ya yi wa Manzo sallama, Sannan mustahabbi ne ya je "Bakiyya"domin ya yi sallama ga shahidan da a ka rufe a wajen.
A nan zamu takaita da wannan abin da muka kawo dangane da wannan al'amari mai son Karin bayani dangane da haka, sai ya koma zuwa ga "Risalar da muka rubuta a kanhaka a cikin harshen larabci.

Ziyarar Kabarin Manzo A Mahangar Kur'ani Da Sunna
A: A Mahangar Kur'ani Mai girma
Kur'ani mai girma yana bai wa al'ummar musulmi umarni da su je wajen Manzo su nemi gafararsa sannan su nemi Manzo (s.a.w) don ya nema musu gafarar Allah madaukaki: "Duk lokacin da suka zalunci kawunansu (zunubi) idan suka zo wajen Manzo suka nemi gafa kuma Manzon ya nema musu gafar a wajen Allah, lallai Allah mai rahama ne kuma mai karbar tuba. "
A wani wurin ciki Kur'ani Allah madaukaki yana zargin munafukai da cewa duk lokacin da aka neme su da su je wajen ma'aiki don ya nema musu gafara sai su kiya: "Idan a ka ce musu ko zo Manzo ya nema muku gafara, sai su juya fusakunsu (don nuna rashin amincewa) zaka ga suna kin maganarka suna masu nuna girman kai. "
Shehin malamin nan kuma AhlusSunna, Takiyyuddeen Subki, Ya yi imani da cewa: Msuslmi a wannan lokacin ma tare da amfani da wannan aya suna iya zuwa wajen Manzo su nemi gafararsa kuma Allah ya gafarta musu. Ya kara da cewa duk da yake wannan aya ta shafi lokacin da Manzo yake a raye ne, amma neman gafara ta hanyarsa bai kebanta da lokacin da yake a raye ba. Saboda wannan wani matsayi ne wanda aka bai wa Manzo (s.a.w) don haka sakamakon rabuwarsa da duniya wannan matsayi ba zai kau ba.
Mai yiwuwa a ce: Wannan abin da ya zo a cikin wannan aya da muka ambata a sama, ya kunshi nuna matsayi da daukaka ta Manzo ne kawai, amma aiwatar da wannan ya kebanci lokacin rayuwarsa ne kawai, amma ba lokacin da baya duniya ba, ta yadda alakarmu da shi ta yanke.
Amma wannan magana sam ba abin karba ba ce, domin kuwa dalilan da zamu ambata a nan gaba suna bayyana cewa rasuwar Manzo sam ba ta da wani tasiri akan wannan al'amari, don haka mutuwa da rayuwarsa babu wani bambanci duk daya ne:
1-Mutuwa ba tana nuna karshen dan Adam ba ne, mutuwa wata sabuwar kofa ce don shiga wata sabuwar rayuwa kuma duniyar da duk abin da yake a ckinta ya fi abin da yake a duniyar da ta gabata ga rayuwar dan Adam, saboda haka mutum rayayye ne a waccan duniya yana gani kuma yana ji. Musamman shahidai wadanda bayan sun dandana shahada zasu cigaba da karbar ci da sha daga Allah madauakin sarki, kuma suna cikin jin dadi na musamman ta hanyar ruhinsu. Saboda haka zamu yi bayani akan wannan a nan gaba a cikin bahasin rayuwar barzahu.
2-Ya zo da yawa a cikin ruwaya cewa: Salatin da musulmi suke yi wa Manzo akwai mala'iku na musamman masu isar da wannan salati zuwa ga Manzo (s.a.w) don haka duk inda mutum yake idan ya yi wa Manzo salati zai isa zuwa ga manzon. Kamar yadda yake cewa: "Ku yi mani salati, salatin yana isa zuwa gare ni daga duk inda kuke"
3-Musulmi a wajen tahiyar salla an umurce su da su yi wa Manzo sallama, sannan su yi masa gaisuwa, "Assalamu alaika ayyuhan nabiyu warahamatullahi wa barakatuhu" Wannan gaisuwa ba wai kawai an umurci musulmi ba ne da su yi ta zuwa ga Manzo amma shi ba ya jin abin da suke yi, Manzo yana raye kuma yana sauraren mu lokacin da muke yi masa salati.
Wadannan abubuwan da muka fada a sama suna nuna cewa Manzo yana raye a rayuwar barzahu, sannan yana da alaka da mu kuma yana jin abin da muke yi. Sannan yana jin rokonmu kuma yana biya mana bukatunmu a lokacin da ya dace. Saboda haka a nan ya kamata mu ce wadannan ayoyi da muka yi bayani a sama, Suna da ma'ana mai fadi, saboda haka yanzu ma suna kiranmu da ziyarar Manzo a kabarinsa kuma mu nemi gafara kuma ya nema mana gafara ga Allah, sannan mu nemi bukatunmu daga gareshi. Saboda haka ya zo a cikin ziyarar Manzo da ake karantawa a haraminsa cewa mai ziyara ya nemi gafarar Allah ta hanyar manzon tare da kula da ma'anar ayar da muka yi bayani a sama. Saboda haka ziyarar Manzo ba wani abu ba ne sai kawai yin salati ga Manzo da kuma neman bukatu da gafarar Allah ta hanyar mazon. Saboda haka wadanan ayoyi na sama suna iya zama sheda akan inganci da mustahabbacin ziyayarar mazo (s.a.w)
Wata sheda kuma a kan wannan magana ita ce, bayan rasuwar Manzo wani balarabe ya shigo Madina yana karanta wannan aya da muka ambata, sai ya ce: "Na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina kuma ina mai neman ceto gareka zuwa ga Ubangijina"
Sannan muhimmin abu kamar yadda Subki yake cewa: Kiran al'ummar musulmi da su ziyarci Manzo kuma su nemi gafara da bukatunsu daga gareshi wata alama ce ta karrama Manzo da girmama shi. Kuma tabbas wannan girmamawa ba ta kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda girma da mukamin ruhinsa a wajen Allah wani abu ne wanda bai mai shakku a kansa kuma madawwami ne, saboda haka bai kebanta da wani zamani ba sabanin waninsa.
Saboda haka ne malaman Tafisri suka tafi akan cewa, girmama Manzo bai kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda haka dole ne a kiyaye shi har bayan rasuwarsa. Harma ayar da ke umurta musulmi da su rika magana a hanakali a gaban Manzo, tana nan a matsayinta, inda Allah yake cewa: "Ya ku wadanda kuka yi Imani kada ku daga muryarku saman muryar Annabi ".
Saboda haka bai kamata mutum ya rika magana da karfi a cikin haramin mazon mai tsaira ba. Sannan wannan aya an rubuta ta a kan kabarin Manzo, wanda duk ya je wannan wuri ya gane wa idonsa hakan.
B: A Mahangar Sunna
Mun ga hukunci da matsayin Kur'ani akan wannan al'amri yanzu abin da ya rage shi ne ku ga kuma me Sunnar Manzo ke cewa a kan hakan..
Ruwayoyi da dama sun zo akan wannan magana ta ziyarar kabarin Manzo, kuma malamai sun yi kokarin tattara su da kuma tabbatar da danganensu. Saboda haka anan a matsayin misali zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:
1-Takiyyuddeen subki (ya yi wafati a shekara ta756h) a cikin littafinsa "Shifa'us sikam" ya ruwaito hadisi tare da sanadi ingantacce.
2-Nuruddin Ali Bn sahmudi (ya yi wafati 911H) ya ruwaito ruwaya 17 akan wannan magana, a cikin littafinsa na tarihin Madina sannan kuma ya inganta sanadinsa.
3-Muhammad fukki daya daga cikin Malam Azahar tare da shafe sanadi ya ruwaito matanin ruwayoyi 22 akan ziyarar Manzo.
4-Allama Amini tare da tare da bin diddigi wanda ya ci a yaba masa, ya tattara ruwayoyi da dama akan ziyarar Manzo (s.a.w) saboda haka anan kawai zamu yi nuni da daya daga cikin ruwayoyi da ya samo daga littafi 41 da a ka ruwaito a kan hakan. Al-Gadir
Saboda haka kawo dukkan ruwayoyin da danganensu ba zai yiwu ba a nan, saboda haka kawai anan zamu takaita ne da kawo wasu kawai daga cikinsu. Wadanda suke son Karin bayani sai su koma zuwa littafin da aka ambata a sama.
Hadisi na farko: "Wanda duk ya ziyarci kabarina aljanna ta wajaba a gareshi" . wannan hadisi Allama Amini ya ruwaitosa tare da sanadi daga littafi 41.
Hadisi na biyu: Dabarani a cikin mu'ujamul Kabir, Gazali a cikin ihya'u ulum daga Abdullahi Bn umar, Manzo yana cewa: "Duk wanda yazo ziyara kuma saboda kawai ziyarata ya zo, to ya wajaba in cece shi a ranar kiyama. "
Hadisi na uku: Darul kutni ya ruwaito daga Abdullahi Bn umar cewa Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina alokacin aikn hajji, to kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. "
Hadisi na hudu: Darul kutni ya ruwaito daga Bn Umar cewa Manzo (s.a.w) ya ce: "Duk wanda ya ziyarci kabarina kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. "
Anan ya kamata mu yi nazarin matsayin ziyara a wajen Imaman Ahlul-bait (a.s):
Ziyar Manzo A Ruwayar Ahlul-Bait (a.s)
1-Imam Bakir (a.s) yana cewa Manzo (s.a.w) yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni ina raye ko bayan na yi wafati zan kasance mai cetonsa a ranar kiyama"
2-Imam Ali (a.s) yana cewa: "Ku cika hajjinku da manzon Allah a lokacin da kuka fito daga dakin Allah, domin kin ziyararsa rashin girmamawa ne gare shi, an umurce ku da yin hakan. Tare da ziyarar kaburburan da aka umurce ku zaku karashe hajjinku. "
3-Imam Sadik (a.s) daga manzon tsira (s.a.w) yana cewa: "Duk wanda ya zo Makka don aikin hajji amma bai ziyarce ni ba, zan banzatar da shi a ranar tashin kiyama, wanda kuwa ya ziyarce ni cetona ya wajaba a garesa, duk wanda cetona ya wajaba a garesa, aljanna ta wajaba a gareshi. Saduk: Ilalish shara'i'i
4-Imam Sadik (a.s) yana cewa Manzo. (s.a.w) yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni zan zama mai cetonsa a ranar tashin kiyama".
Ruwayoyin da dukkan bagarori guda biyu suka ruwaito ta fuskar ma'ana ba su da bambanci, saboda haka suna karfafa abubuwa guda biyu kamar haka:
A-Duk wanda ya je Makka bai ziyarci Manzo ba, to ya yi wa manzon jafa'i.
B-Duk wanda ya ziyarci Manzo, Manzo zai cece shi a ranmar kiyama. Saboda haka don mu takaita wadannan ruwayoyi guda takwas daga Shi'a da Sunna sun wadatar wanda yake son karin bayani sai ya koma zuwa ga littfan da muka ambata.
Tattaunawar Imam Malik Tare Da Mansur Dawaniki
Kadhi Iyadh ya nakalto tattaunawar Imam Malik tare da Mansur Dawaniki kamar haka:
Mansur Dawaniki wanda yake khalifa ne mashahuri na Abbasiyya, wata rana ya shiga haramin Manzo yana magana da karfi.
Malik a lokacin shi ne Fakih a Madina sai ya juya zuwa ga Mansur ya ce: Ya kai shugaban Muminai, kada ka daga muryarka a cikin wannan masallaci, Allah madaukaki ya koya wa wasu muatane ladabi inda yake cewa: "Kada ku daga muryarku saman muryar Annabi"
Sannan ya ya bi wasu gungu daga cikin mutane ya ce: Lallai wadanda suke kasa da muryarsu a gaban manzon Allah, su ne wadanda Allah ya jarabba zukatansu da takawa"
Sannan Allah yana cewa Wasu gungun mutane wadanda suke hayaniya a bayan gidan Manzo suna cewa: Ya Muhammad ka yi sauri ka fito daga cikin gida, Allah yana kaico da halinsu, yan cewa: "Lallai wadanda suke kiranka daga bayan gida mafi yawansu ba su da hankali".
Sannan ya cigaba da cewa girmama Manzo a lokacin da ba shi da rai kamar lokacin da yake da rai ne babu bambanci.
Lokacin da Mansur ya ji wannan magana sai ya zo da kansa wajen Malik ya ce: A lokacin da nake addu'a zan kalli kibla ne ko kuwa kabarin Manzo?
Sai Malik ya ba shi amsa da cewa: Me ya sa zaka juya wa Manzo baya alhali kuwa shi ne tsaninka kuma tsani ga babanka Adam har zuwa ranar tashin kiyama, don haka ka kalli kabarin Manzo ka nemi ceto daga gare shi Allah ya amshi cetonka. Allah yana cewa: A lokacin da suka zalunci kawunansu suka zo gare ka suna neman gafarar Allah manzon zai nema musu gafara..".
Ziyarar Kabari Da Kiyaye Asali
A cikin wannan Bahasi namu mai tsawo kawai mun yi amfani ne da ruwayoyin da suke nuni akan wannan al'amari daga ruwayoyin Ahluls Sunna. Amma muna da ruwayoyi da dama daga maruwaitanmu na Shi'a da suka ruwaito daga Imaman Ahlul baiti (a.s). Wadanda ba mu yi nazari akansu ba. Sdaboda haka idan aka duba Littattafan hadisai na Shi'a za a tabbatar da wannan al'amari cewa, ziyarar Manzo da Ahlul baiti (a.s) yana daga cikin abin da yake karbabbe ga kowa a cikin wannan mazahaba ta Ahlul baiti (a.s) sakamakon haka ne aka rubuta littfai da dama akan hakan wadanda a ka fi sani da suna "almazar" wato wurin ziyara, daga cikin wadannan littfai kuwa wanda duk ya fi shahara shi ne, "Alkamil Ziyarat" wanda shehin malamin nan mai suna Ja'afar Bn muhammad Bn kulawaihi ya rubuta. (ya yi wafati 367H).
A nan zamu kara da cewa, kiyaye abubuwan da suke na asali yana daya daga cikin ayyukan addinin musulunci. Abin da muke nufi da asali kuwa shi ne abin da yake bayyanar da gaskiyar musulunci da cigabansa har ya isa zuwa ga dukkan zamunna.
Addinin musulunci addini ne da yake na duniya baki daya, don haka har zuwa tashin kiyama zai kasance matsayin addini cikakke har karshen duniya. Saboda haka dole ne mu yi iya koarinmu mu ga cewa mun kiyayen asalimn wannan adini don ya isa kamar yadda ya zo zuwa ga wadanda zasu zo a nan gaba.
Saboda haka ziyarar kabarin Manzo da Ahlul baiti (a.s) yana daya daga cikin kiyaye asalin addini, don haka barin hakan bayan wani tsawon zamani sai ya zamana an manta da wannan babban aiki mai albarka. Saboda haka dangane da wadanda zasu zo nan gaba sai a zamana wadannan wurare na musamman na manyan bayin Allah ya koma kamar wani abin tatsuniya.
Kasancewar zuwan Isa (a.s) a yau wani abu ne wanda ba abin shakka ba ga al'ummar musulmi, amma a yammacin duniya musamman ga matasa al'amarin Annabi Isa ya zama kamar wani abin tatsuniya, wannan kuwa ya faru ne sakamakon rashin wani abu wanda yake nuna gaskiyar samuwar shi Annabi Isa (a.s) a hannayen muatane. Wannan kuwa ya faru ne sakamakaon canza littafinsa da a ka yi, don haka dangane da shi kansa Masih da mahaifiyarsa da sauran manyan sahabbansa babu wani abu na hakika wanda yake tabbas daga garesu ya ke. Don haka sakamakon tsawon zamani a yau al'marin masihiyya ya zamana kimarsa ta rage kuma ya shiga cikin wani halin kokwanto da rashin tabbas. Kamar yadda a yau ziyarar Manzo wadda take daya daga cikin abu na asali a cikin addinin musulunci kuma mai nuna hakikanin matsayi da samuwar Manzo tana neman ta zama wani abu marar muhimmanci a cikin al'ummar musulmi, koma ya zamana an ajiye ta a gefe guda. Don haka sakamakon tsawon zamani akwai yiwuwar abubuwan asali na addinin musulunci da waliyyan Allah, su shiga cikin wannan hadari mai girma.
Saboda haka al'ummar musulmi dole ne su tashi tsaye domin kare wannan hadari da ya fuskanto su, wannan kuwa yana samuwa ne ta hanyar kiyaye duk wani abu da ya shafi sakon manzanci da Imamanci, ta yadda za a rika tuna shi a kowane zamani. Saboda haka ziyarar wadannan manyan bayin Allah tana daya daga cikin hanyoyin kiyaye su daga bacewa da kuma yin tunani a kansu a kowane lokaci. Saboda haka sakamakon yin kahan ba za a taba watsi da matsayin wannan muhimmin al'amari ba, ta yadda za iya kulle kofar ganawa ta hanyar ruhi da wadannan manyan bayin Allah ga al'ummar musulmi.
Saboda haka da ikon Allah a nan gaba zamu yi magana akan kiyaye wadannan wurare masu tsarki.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012