Musulmi a Yau
  • Take: Musulmi a Yau
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 21:3:38 13-9-1403

MUSULMI A YAU

Da SunanSa Madaukaki Amincin Allah ya tabbata ga Annabi da Alayensa
MUSULMIN DUNIYA Idan muka dauki musulmi muka dora su a sikelin rahamar ubangiji kan talikai sai mu ga sun yi hannun riga da wannan! Sai wani bangare tun farkon tarihin wannan addini suka riki gaba da gidan Manzon Allah (s.a.w), kuma guggubin wannan koyarwar ta sanya kyamar yabo ko nuna matsayin Annabi (s.a.w), kuma a yau ta haramta tawassuli da shi ko yin bukin murnar haihuwarsa.
Mafi munin ayyukan wannan tunani da yake yaduwa a duniya cikin wadannan shekaru 30 na karshe shi ne kokarin rarraba kawukan musulmi. Idan ya ga dan Sunna yana riko da mazhabar da ba tasa ba, yana tunani da ya saba wa nasa musamman idan yana riko da darikun waliyyai ne, to sai ya kira shi mushriki. Idan ya ga dan Shi'a sai ya kira shi kafiri, ko ya jingina masa kin sahabbai.
Su wadannan mutane su ba Sunna ba, su kuma ba Shi'a ba, amma sun fi kowa da'awar su suke riko da Sunna. Wallahi da sun yi riko da Sunna da sun riki wasiyyar Manzon Allah (s.a.w) ga al'ummarsa ta yin riko da littafin Allah da Ahlin gidansa kamar yadda ya zo a hadisai mutawatirai gun Sunna da Shi'a duka. (Koma wa; Muslim, Mustadark, da Masnad Ahmad d.s.s).
Wannan akida mai kiyayya da koyarwar wasiyyar Annabi (s.a.w) babu wani sakamako da ya yi wa Annabi (s.a.w) sai bata surar sakonsa a idanun duniya, har ma ya kasance idan ka ji sunan ta'addanci a yau to tunanin yamma yana kallon musulunci ne. Ba don komai ba, sai domin wannan tunanin ba shi da wani aiki sai kira ga rarraba ko kashe bayin Allah, ya sanya bamabamai a masallatai, an sanya wa kananan yara da mata, an sanya a makarantu, babu wani mutum da ya tsira, babu musulmi balle waninsa.
Don haka ne muke ganin wautar masu jingina ta'addanci ga musulunci, alhalin suna ganin wannan Akidar hatta da Manzon Allah da ya zo mana da sako yana ganinsa kamar ambulan ne na wasika. Don haka masu kiran musulunci da ta'addanci a yammancin duniya ba su yi masa adalci ba, domin ko musulmi bai tsira daga wannan ta'addancin ba! Sannan kuma idan ma'abota wasu addinai suka yi ta'addanci don me ba ma ganin an jingina shi ga addininsu. Ta'addanci fa yana nan ta'addanci, ko daga musulmi a maiduguri -da ya harbe wanda bai ji ba bai gani ba kamar yadda Jazira suka nuna shi, ko kuma wanda ya kashe dan sanda mai bayar da kariya ga al'ummar kasa- ko daga Kirista da yake garin Jos! duk sunansa Ta'addanci.
Wannan ra'ayin yana ganin saba masa a tunani da akida yana nufin batan daya bangaren ne, don haka yana ganin dole ne fahimtarsa ta kasance kowa ya yi riko da ita, idan ba haka ba kuwa to sauran bangarorin ba musulmi ba ne. Sakamakon wannan ra'ayi yana dauke da wannan fikira da akida, don haka ne ya kasance a kullum ba shi da wani kira sai neman kashe musulmi. Zaka ji mai dakon wannan tunanin bai sanya komai gaba ba sai kiran rarraba da zubar da jinni, zaka ji shi a radio da talabijin yana maimaitawa kamar Aku. Yana mai maimaitawa cewa ya kamata a dauki mataki kan masu tunani kaza, kai ya kamata a kashe masu kaza, masu kaza kafirai ne, babu wasu kalmomi na rahama a cikin wannan tunani ko kwarzane.
Abin takaici yadda wannan ra'ayin ya rudi wasu masu da'awar son gidan Annabi (s.a.w) suna masu gafala ba su san abin da yakan kai ya komo ba, sai suka yi dakon irin wannan tunanin na rarrabar musulmi kyauta ba su sani ba. Babu wani aiki na cutar da musulunci da musulmi a yau irin gaba da jefa kiyayya tsakanin al'ummar musulmi ko jefa gabar wata jama'a saboda kawai tana da wata fahimta, balle a ce wannan jama'ar musulma ce.
A daidai lokacin da ya kamata hatta da kirista da masu bautar gumaka mu kira su, mu ja su a jiki, domin mu sanar da su sakon Manzon Allah (s.a.w), sai ga wasu babu wani abu da suka sanya gaba sai rura wutar gaba tsakanin musulmi da gaba da koyarwar gidan Manzon Allah (s.a.w), suna masu tayar da jijiyar wuya sai sun rarraba musulmi.
A yanzu ba abin mamaki ba ne kirista ta yi shekaru 35 a cikin birnin Kano amma ba ta taba sanin matsayin musulmi game da Annabi Isa (a.s) ba?! A yanzu muna ganin da Manzon Allah (s.a.w) ya kasance haka zamu samu labarin ma wannan rahamar sakon nasa ko da a rubuce a tarihi? Sannan muna haka muke tsammanin samun tsira!
A yanzu jahiltar addinin musulunci da hadafinsa da shi kansa musulmi yake a kai laifin waye?! Sai aka bar fagen addini ga kowane mai magana, sai malamai suka yarda suka zubar da kimar matsayinsu, sai ka ga hadisai ana wasa da su. Kwanan nan ne na ga wani yana fassara hadisin a yi aure a hayayyafa yadda ya ga dama, babu wata diraya, ba tare da ya san yana da alaka da zamani, da wuri, da yanayi ba. Shi dai yana batun a hayayyafa da yawa, a watsa 'ya'yan, titi ya yi musu tarbiyya, ban sani ba ko yana ganin Annabi zai yi alfahari da tarbiyyar titi.
Sai kowane mutum ya zama malami ko da bai kware da karatu a fagen ilimin addini ba, matukar ya iya buda baki ya yi magana to yana da mahanga a addini. Babu wani fagen ilimi kamar likitanci, ko kimiyya, ko rayuwar halittu da ake yi masa katsalandan ko cin zarafi irin fagen addini. Abin takaici hatta da wanda ya rayu a titi yana rigaita yana da mahanga a addini saboda reni ga addini. Sannan karancin wayewa da fadada tunani daga malaman kansu ta sanya ba su da ta cewa; a fagage masu yawa, sai suka wakilta wannan a hannun masu tunanin yamma domin su cike wadannan fagage.
Yaya ake tsammanin Musuluncin da ake nuna wa duniya a yau cikin ayyukan ta'addanci da sunan musulunci zai samu karbuwa a yammacin duniya. Musulunci bai taba yarda ka kame wani ko kashe shi babu dalili na shari'a ba, kuma wannan ba ya hannun kowa sai hukuma, ita ma hukuma dole ne ya kasance bisa adalcin dokokinta.
Sannan duk wanda wata kasa ta ba shi izini domin ya shiga cikinta to yana da kariyar da babu wani mai hakkin taba shi ko mai kuwa munanan ayyukansa, kamar yadda duk wanda aka ba shi izini don shiga wata kasa, musulunci bai yadda ya saba wa alkawarin da ya dauka na bin dokar wannan kasa ba, balle kuma ya kai ga cin mutunci ko zubar da jinin jama'arta. Don haka ne musulunci ya barranta daga dukkan munanan ayyukan da ake yi da sunansa ana bata masa suna!.
Musulunci ya yi mana tarbiyyar kira da kalma mai taushi ko da ga mafi kafircin mutane ne: "… Ku gaya masa magana mai taushi…" (Taha: 44), ta yadda hatta da Fir'aunan da ya yi da'awar Ubangijintaka amma sai Allah ya yi umarni ga annabi Musa (a.s) da ya gaya masa magana mai taushi, balle kuma mutanen da ba su ji, ba su gani ba.
Ba mu ce sauran addinai ba su da mabiya masu ta'addanci da sunan addinin ko da wata manufa ba, sai dai mu musulumi abin takaici ne a cikinmu a samu masu yi, kuma mafi muni a jingina wannan fahimta da musulunci alhalin abin da masu wannan tunanin suke yi ya yi hannun riga da koyarwar musulunci a fili.
Mu koma wa tarinin musulunci mu ga sakon Annabi (s.a.w) da ya bayar da kariya ga dukkan masu addinan sama, sai bayahude da kirista suka zauna a cikin daular musulunci a cikin mafificin aminci da babu kamarsa a tarihi, ba mu taba ganin musulunci ya taba wani ba sai wanda ya taba shi.
Kuma sau da yawa mun ga hakurin musulmi duk da suna da karfi da iko amma sai masu wani addini ya yi musu isgili su jure, mu duba imam Bakir (a.s) jikan Manzon Allah (s.a.w) da isgilin da wani kirista ya yi masa. Imam Muhammad Bakir (a.s) ya kasance ma'abocin fifiko, da daukaka, da addini, da ilimi mai yawa, da hakuri mai yalwa, da kyawawan halaye, da ibada, da kaskan da kai, da baiwa, da rangwame.
Ya kai karshen kyawawan dabi'u wani Kirista ya ce masa: Kai bakar ne. (wato; saniya), Sai ya ce: Ni dai Bakir (Mai tsage ilimi) ne. Sai Kirista ya ce: Kai dan mai dafa abinci ne. Sai ya ce: Wannan aikinta kenan. Sai Kirista ya ce: Kai dan bakar mace ne ballagaza. Sai ya ce: Idan ka yi gaskiya Allah ya gafarta mata, idan ka yi karya kuma Allah ya gafarta maka. Sai wannan Kirista ya musulunta!
Muna iya ganin yadda wannan mutumin ya kai matukar keta hurumi da cin mutuncin Uwa ta wannan Imami mai girma amma sai ya jure ya yi irin halin kakansa, sai ga shi sakamakon haka wannan Kiristan ya musulunta!.
Kissoshin Annabi (s.a.w) da wulakancin da wadanda ba musulmi ba suka yi masa, da juriyar da ya yi suna da yawa, kuma sun nuna mene ne musulunci, kuma da yawa sun musulunta saboda haka. Kada mu manta fa a wannan lokacin da yake jure wannan wulakancin shi ne shugaban daular musulunci, amma sai ya jure domin ya kasance rahama ga talikai, haka nan wasiyyansa suka yi irin wannan juriya tasa suka kasance rahama ga talikai. Don me mu ba zamu samu yin kyakkyawan koyi da shi ba, don me mu ba zamu nuna wa duniya hakikanin musulunci ba!
Wani Kiristan arewacin Nijeriya (ta tsakiya) yana jin an zalunce shi a tarihin rayuwarsa, kuma yana jin musulunci ne ya yi masa, don me musulmi ba zasu wayar da kansa ba ya gane cewa babu wani musulunci da ya zalunce shi. Ya san cewa idan an zalunci ne da sunan musulunci to lallai an zalunci musulunci ne kawai. Kuma ya gane cewa ba shi kawai aka zalunta a tarihi ba, musulmi ma an yi masa wannan zaluncin. Idan kuwa ba a zalunce shi ba to don me yake ganin an yi masa zalunci a tarihi!? Idan kuwa an zalunce shi ne, to yana nufin shi kuma abin da yake yi yau kan musulmi yaya sunansa!?
Mu zauna a teburi daya da mai matsala da mu, mu san meye matsalar, idan muka ga muna da kuskure sai mu ba shi hakuri mu nemi yafewa, sannan sai mu kulla zumunci da shi; A bayanin Malam Kira'ati; ranar alhamis 17, ga Rabi'ul Awwal, 1431, yana raddi ga masu sukan daular musulunci yana cewa: "Idan ka ce: Akwai aibi a daula haka ne, kuma neman cewa babu wannan aibin kuskure ne, amma cewa ta rushe saboda akwai aibi laifi ne babba mai girman gaske. Babban abin nuni da shi a nan cewa mai aibi bai kamata ya yi musun aibin ba, amma shi kuma mai cewa; akwai aibi ba yana nufin ya rusa abin da yake gani da aibi ba, sai dai ya nemi gyara.
Musulunci ya yi furuci da cewa kirista da bayahude suna da addini, sai dai a yi bahasi da su da hikima da kyautatawa domin dauke rashin fahimta da suke ciki, ya kira su da zama tebure daya domin karfafa juna da bin abin da suka yi tarayya a ciki, da tattaunawa cikin hikima a inda suka yi sabani yana mai cewa: "Ka ce: Ya ku ma'abota littafi ku zo zuwa ga kalma madaidaiciya a tsakaninmu da ku…" (Aali Imrana: 64). Da fadinsa: "Kada ku yi jayayya da ma'abota littafi sai da wacce take ita ce mafi kyau…" (Ankabut: 46).
Kamar yadda ayoyi masu yawa suka zo suna masu karfafa imanin musulmi da dukkan annabawan Allah da dukkan littattafansu. Kuma tarihi ya nuna yadda musulunci ya girmama dukkan addinai saukakku ya mutunta musu tunaninsu. Sai dai an samu rashin fahimta tsakaninsu a tarihi wanda jahiltar juna ya haifar da shi, kuma wannan bala'in a yanzu haka ya fi da kamari. Ba komai ya haifar da yakin 'yan mishan a kan daulolin musulmi ba shekaru 500 da suka gabata sai wannan rashin fahimtar juna. Kuma wannan ya samo asali ne daga kauce wa koyarwar wadannan ayoyin da suke sama.
Sannan mafi girman takaitawa tana gunmu da muke da wannan tsarin saukakke daga Allah da ba mu isar da shi ba yadda ya dace, sai aka wayi gari mu mun ki tsayawa mu fahimci sakon da kyau saboda mun dauka kamar gado yake, balle wadanda ba musulmi ba da su ma ba su san sakon ba. Sai dai har yanzu ba mu yi lati ba, masu hankali da ilimi daga cikinmu ya kamata su karanci abin su san inda zasu fara domin isar da sakon rahamar ga dukkan talikai.
Mafi girman abin da ya kai mu ga fadawa cikin wannan halin bai wuce rashin fahimtar musulunci ba, da kyakkyawar koyarwar da ya bari cikin biyayya ga Kur'ani da Alayen Manzon Allah (s.a.w). Sai aka yi nisa da Kur'ani mai girma da koyarwarsa, Alayen Muhammad (s.a.w) kuwa aka yi watsi da su, ba ma kawai an yi watsi da su ba ne, sai da aka yi wa al'umma mummunar tarbiyyar kyamar Annabi (s.a.w) da Alayensa, sannan kuma aka kyamaci koyarwarsu.
Kuma abin takaici wannan lamari ya yi muni har zuwa yau, ta yadda hatta da fadar abin da ya faru kansu laifi ne, mafi muni shi ne yabon wadanda suka yi musu kisan kare dangi irinsu Yazid dan Mu'awiya, sannan kuma kyamar mazhabarsu da yi mata bita-dakulli. Masu jin cewa da suna raye aka kashe Alayen Annabi (s.a.w) da zuriyarsu da sun ba wa sarakuna tasu gudummuwa, sai suka ga bari su bi mabiyansu da takurawa da kashewa, don haka sai suka sanya dukkan karfinsu wurin gaba da mabiyansu da tafarkinsu.
Wani mutumin Sham ya ga Imam Hasan (a.s) yana haye kan dabba, sai ya rika la'antar imam Hasan (a.s), shi kuwa Imam Hasan (a.s) bai yi masa raddi ba. Yayin da ya gama sai Imam Hasan (a.s) ya zo wajensa ya yi masa sallama ya yi dariya ya ce: Ya kai wannan tsoho ina tsammanin kai bako ne a wannan gari, ta yiwu ka yi batan kai. Amma da ka roke mu da mun ba ka, kuma da ka nemi shiryarwarmu da mun shiryar da kai, da ka nemi mu hau da kai da mun ba ka abin hawa. Idan kuwa kana jin yunwa ne to sai mu ciyar da kai, idan kuwa kana da tsaraici ne to sai mu tufatar da kai, idan kuwa kana da talauci ne sai mu wadata ka, idan ka kasance korarre ne sai mu ba ka wajen zama, idan kuwa kana da wata bukata ne sai mu biya maka. Yayin da mutumin nan ya ji wannan magana sai ya yi kuka ya ce: Na shaida kai ne halifan Allah a bayan kasa, Allah ne kawai ya san inda yake sanya sakonsa. ( Manakib: Mujalladi 4, shafi: 19).
Wannan shi ne jikan Manzon Allah (s.a.w) na farko imam Hasan dan Ali da Fadima (a.s), amma Mu'awiya dan Abu Sufyan ya tarbiyyantar da al'umma kan kin su, sannan ya sanya matar Imam Hasan (a.s) ta sanya masa gubar da ta kashe shi, sannan ya wajabta la'antar dan'uwan Manzon Allah -kuma baban Hasan wato Imam Ali da yake baban zuriyar Annabi (s.a.w)- a kan mimbari da ake kiran wannan la'anar da Sunna har tsawon shekaru tamanin sai a zamanin halifancin Umar dan Abdul'aziz sannan ya hana wannan Sunna -ta la'anar Imam Ali- da aka sanya mata hadisai masu nuna falalarta.
Sannan ga yunkurin cire shaidawa da manzancin Manzon Allah (s.a.w) a kiran salla da shi ma bai ci nasara ba. Amma duk da haka sai ga al'ummar musulmi ta karbi wannan tafarkin sai 'yan kadan da Allah ya yi wa ludufinsa. Don haka ya hau kan al'ummar musulmi su tashi tsaye domin fahimtar meye musulunci sahihi da Annabi ya zo da shi, wanda yake wajabta girmama Annabi (s.a.w), da riko da Kur'ani da Alayen Annabi (s.a.w), wanda ya fadi sunansu da kansa da cewa su sha biyu ne bayansa.
Ta yiwu wani ya ce: Duk da mun san cewa; Annabi (s.a.w) ya bar mana halifofi kuma imamai jagorori sha biyu ne, amma ai littattafai kamar Muslim da sauransu sun fadi adadi ne kawai amma ba su kawo sunayen ba?
Sai mu ce: Alayen Annabi (s.a.w) sun ruwaito su waye da sunayensu. Sannan kuma shin akwai wani mai hankali da zai bar wani abu muhimmi da cewa na wasu ne bayan mutuwarsa, sannan sai ya yi shiru bai fadi su waye ba?! Balle addinin Allah madaukaki da yake makomar shiriya har tashin kiyama! Ko kuma an boye su ne saboda kawai suna Alayen Manzon Allah!? Ko kuwa akwai wani wanda zai iya kawo su a lokacin da hukuncin hakan yake nufin fille wuyansa?! Ko ba mu gani ba ne cewa; sanya sunan Ali kawai a wancan zamanin yana iya kaiwa ga hukuncin kisa?!
Yana da muhimmanci matuka mu koma wa tarihin Annabi (s.a.w) da daulolin da suka zo bayansa domin sanin makomar musulunci da musulmi bayansa, kamar dai yadda yahudawa da nasara suka kasance bayan annabawa, sai maganar Manzon Allah (s.a.w) ta gaskata cewa; al'ummarsa sai ta bi abin da suka yi taku-da-taku. Don haka mu yi hattara! mu san muna da nauyin amanar sakon Manzon Allah (s.a.w) a hannunmu. Kuma idan muka kiyaye to mu muka amfana, idan kuwa ba mu kiyaye ba, to ba zamu cutar da Allah da komai ba!.
Manzon Allah da Alayensa (a.s) sun yi mu'amala da wadanda ba musulmi ba kyakkyawar mu'amala fiye da ta sarakunan musulmi da aka yi a dauloli. Don haka ne ma zamu ga hatta da Kiristoci sun tausaya wa Alayen Manzon Allah (s.a.w) a lokutan wadannan dauloli fiye da yadda musulmi kansu suka tausaya musu. Hasali ma musulmin ba su tausaya musu ba sai 'yan kadan daga ciki, kissoshin kisan kare dangi da aka yi musu lokacin sarakuna musamman irinsu Yazidu da Harunar Rashid ba boye suke ba. Bincika ka ga tarihin rashin imanin da ba a taba yin sa ba a tarihin dan Adam. Duba littattafan tarihi da musulmi suka rubuta kamar Makatilul Talibiyyin.
Don haka muna da aiki babba a gabanmu, mu koma cikin hayyacinmu, mu nisanci dimuwa, mu yi aiki da wasiyyar Annabi ga wannan al'umma, mu so juna, mu hade wuri daya, mu nuna wa duniya hakikanin sakon Annabi (s.a.w), da wannan ne Annabi zai yi farin ciki da mu a mauludinsa. Amma mu yabe shi mu fadi rayuwarsa, sannan kuma a aikace mu saba mata gaba daya, kamar muna isgili ne ma.
Malamai su bar neman duniya da hassada ga juna, su shagaltu da neman mafita ga wannan al'umma. Shugabanni su farka daga gafalarsu, su nisanci kyamar al'umma da barnar dukiyarta, su tausaya wa al'umma da idanun rahama. Mutane kuwa su so gaskiya su kawar da jahilcinsu, su nisanci kiraye-kirayen gaba da juna, da rikicin jahilci, su zauna da juna da kyawawan halaye. Idan muka kiyaye zamu samu rahamar Manzon Allah (s.a.w), in kuwa ba haka ba, duk abin da muka gani mu zargi kawukanmu.
Amincin Allah (s.w.t) ya tabbata ga wadanda suka bi shiriya!
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Thursday, March 11, 2010