Su waye shugabannin gidan aljanna?
  • Take: Su waye shugabannin gidan aljanna?
  • marubucin:
  • Source:
  • Ranar Saki: 4:26:5 21-8-1403

Bayani a takaice:

Imam Hasan da Husain jikokin manzan Allah (saw) shawagabannin ne ga dukkanin ‘yan aljanna kuma su shugabannin samarin gidan aljanna ne. amma shugabancin su ya fi karfi kan samarin da suka yi shadan a lokacin samrtarsu, kuma wannan bai ci karo da shagabancin sauran manzanni da Annabawa a cikin gidan aljanna ba.
A dunkule, bisa la’akari da dalilai wannan na nuna cewa shugabancin wadannan imamai biyu ga dukkanin samarin gidan aljana bai hada har da sauran Annabawa da Manzanni ba.

 

Bayani filla-filla

Manzanni da waliyyai shugabanni ne ga ‘yan digan aljanna kamar yadda Imam Hasan da Husain na daga cikin wadannan shuwagabanni. Gabaki dayan manzanni da waliyyai na da matsayi sama da na sauran yan’gidan aljanna. Amma wani lokaci Allah  ya kan kebanci wasu da wani matsayi na musammani ya ba su wani mukami da zasu kebanta da shi kuma su shahara da shi.
Idan har ana kiran sayyida fadima da “shugaban matan gidan aljanna” kuma ana kiran imami na hudu an yi masa lakabi da “shugaban masu bauta” da “shugaban masu sujjada”, wannan ba ya nifin cewa fadima (as) ba shugaba ce ga maza ba, kuma wannan baya nufin imam sajjad ba shugaba ne ga wadanda ba sa yawaita ibada da sujja ba. Illa iyaka saboda kasantuwar sayyida fatima mace ce da kuma yadda imam sajjad ya zama ya shagaltu da yawan ibada da sujjada a lokacin da makiya suke kewaye da shi suka hana shin ayyukan cigabatar da jama’a da al’umma, sai wannan ya sa ya cancanci wannan lakabi.
Bisa wannan ba za mu iya yin tambaya kamar haka ba mu ce: tun da an yiwa Imam sajjad lakabi da mai ibada da sujjada: kenan ya zama shi ne shugaban masu sujjada baki daya har ma da kakanninsa manzon rahama (saw) da imam Ali kenan? Kuma su ba shuwagabanni ba ne a wannan fagen ba?
Don haka shugabanci Imam Hasan da Husain kan samarin gidan aljannan a bisa irin wannan mahangar ne shi ma, saboda wadannan bayin Allah  a lokcin da musulunci yake farkon zuwa aka haife su kuma kwanakin samartarsu ya hadu da kwanakin samartar musulunci, kuma sun kasance a lokacin da suke samari a lokocin rayuwar manzo da ma bayan samartakarsu a tsakatsakin musulmai ba a sami wasu samari da su ka kai kusa da matsayinsu a fagen takawa da girma ba, don haka suka zama sun cancanci wannan lakabi sai suka zama shuwagannin samari da tsofaffin gidan aljanna.
Domin karfafa wannan bayani da ya gabata zamu kawo muku ruwayoyi guda biyu:
1.    An karbo daga imam sadiK yana cewa ”ku ziyarci kabarin Husain (as) kada ku kaurace masa hakika shi ne shugaban samarin aljanna kuma sugaban samari shahidai.  
Bisa la’ajari da wannan ruwayar zamu ga cewa imam Husain ya shahara da wannna lakabi na shugaban shahidai duk da cewa ya yi shahada a lokacin da yake manyanta, lakabin shugaban samari shahidai kuma na nuni bisa kulawar imam ta musamma ga wadanda suka yi shahada a shekarun samarta,  
2.    An karbo daga imam Ali (as) yana cewa manzon Allah  ya ce wani mala’ika ya zo min yana cewa: wani mala’ika ya zo min sannan ya ce da ni ya Muhammad hakika Allah  ta’ala yana cewa da kai: na umarci bishiyar duba da ta dauki durri da yakutu da murjani sannan ta warwatsu kan duk wadanda suka halarci auren fadima na daga mal’iku da hurul ini, kuma lalle sauran mazauna sammai sun yi murna da haka kuma hakika zasu haifi ‘ya’ya biyu shugabanni ni su a duniya kuma da sannu zasu zama shuwagabannin tsofaffi da samarin gidan aljanna kuma hakika za a cika ajanna da ado a sakamakon haka ka yi farinciki ya kai Muhammad hakika kai ne shugaban na farko da na karshe.  
A wannan ruwayar ma akwai manuniya kan cewa su shawagabbanin gidan aljanna ne amma la’akari da cewa a cikin aljanna babu tsofaffi kuma ba a tsufa. Don haka a dunkuke zamu iya cewa wadanna jikoki na ma’aiki shuwagababbin ne na dukkanin mutane gidan aljanna kuma amma wannan shugabancin an kalle shi ta bangaren wadanda suke samari suka bar duniya shahidai ko kuma suka rasu, kuma wannan bayanin bai saba da kasantuwar dukkanin ‘yan aljanna samari ne ba, kuma abin da ake nufi da tsofaffin su ne wadanda suka bar duniya bayan sun tsufa.
Wata tambaya da zata iya zuwa kwakwalwa it ace: la’akari da wannan hadisi shin yana nufin Imam Hasan da Husain su shuwgabannin sauran Annabawa da Waliyayyi ne kenan?  Wanda za a iya bada wannan amsa a takaice kamar haka: dukkanin wata Magana tana da togaciya wacce wani lokaci togaciyar ta kan zo a cikin wannan maganar, wani lokaci kuma tagaciyar kan dogara da wani dalili bayyananne, wanda ba bukatar a yi wani dogon bayani kansa.
Bisa wannan asasi abin da za a iya fahimta a nan shi ne shugabancin wadannan imamai biyu kan dukkanin yan aljanna ne, ba kan daidaiku kamar Manzo (saw) imam Ali da sayyida fadima (as) dss ba.....
Zamu iyan karfafa wanna maganar da ruwayar nan mai zuwa wacce ta yi kama da abin da muke Magana a kai.
Wani mutun ya tambayi imam sadik cewa shin da gaske ne mazon Allah (saw) ya ce Abuzarri ne mafi gaskiyar mutane sai imam sadik ya ce masa haka ne, sai ya ce to ina manazun Allah da imam Ali suke?  sannan ina Imam Hasan da Husain? Shin wannan yana nifin Abuzarri ya fi su fadar gaskiya? Bayan da imam ya yi wasu bayanai sannan sai ya ce mu Ahlubaiti ba a sawa da mu cikin irin wannan kiya sin.
Wannan na nifin bisa la’akari da dalilai da abubuwa na sarari zaka iya fahimtar cewa fadin gaskiyar Abuzarri an kwatanta shi ne da sauran mutane ba da Ahlulbaiti (as) ba, duk da cewa babu wannnan bayain dalla-dalla a cikin ruwaya.

na fassaro wannan makala daga site din islamquest.net

Munir Muhammad Said
ALKANAWI