Gadir a Sabon Tufafinsa
  • Take: Gadir a Sabon Tufafinsa
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 16:13:34 13-10-1403

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
GADIR A SABON TUFAFIN ZAMANI Wannan bayani kan Gadir an rubuta shi sakamakon gasa da aka yi ta rubutun makala kan Gadir a makarantar Imam Khomain da take Bajak-Kum, ta kasar Iran, a shekarar 1423 H. Kuma mutane 128 ne daga kasashe sama da 50 na duniya da suka hada da latin Amurka, da Amurka, da Asia, da Turai, da Afrika ne suka yi rubutu kan Gadir a wannan gasar, Godiya ta tabbata ga Allah da ni daga Nijeriya na samu wanda ya cinye a matsayin na farko. Duk da na rubuta bayanin da larabci ne, kuma ya fi dadi da larabcin, amma na fassara shi zuwa harshen Hausa kamar haka:

Da Sunansa Madaukaki
Lokacin da na karbi littafin hudubar Manzon Allah (s.a.w) a yau litinin 22 ga watan zalhijji 1423 bayan na duba sai na ga cewa dukkan matsalar dan Adam ta duniya da kuma dukkan kamalar dan Adam yake nema ta lahira da dukkan abubuwan da suka faru ko suke faruwa ko zasu faru a tarihin rayuwar dan Adam duk sun damfaru da wannan huduba kuma warwararsu ta ta'allaka da fahimtar wannan huduba da abin da ya gudan a wannan rana mai girma ta Gadir.
Ina iya cewa har a cikin zuciyata na yi imani cewa har da matasalarmu ta kashin kanmu wato ba kawai matsalar al'umma ba, warwararta tana dogara bisa imani da abin da yake kunshe cikin wannnan sako na Ubangiji da ya aiko fiyayyen mazajen Allah kuma bayinsa na gari da shi.
Da na kalli hudubar da kyau sai na ga gabatarwarta ita ce ainihin karshenta, wato; farkonta da tsakiyarta wadanda su ne madarar sakon da ke kunshe cikinta, da kuma karshenta duka abu guda ne, domin dukkan su sun hadu domin fitar da hikimar samuwar mutum a bayan kasa, da hadafin halittarsa, da kuma abubuwan da zai kudurce a zuciyarsa domin samun tunani sahihi. Wadannan abubuwa ne da idan suka gyaru suka zama su ne suke motsa mutum a tunani da ayyukansa sai a gan shi yana motsawa zuwa ga neman kamala a aikace, sai ka ga ayyukansa sun zama irin na mutum kamili wanda shi ne darasin da waccan hudubar take dauke kuma take kunshe da shi .
Mu duba sosai da mai ganin mai basira zamu ga abin ta kunsa bayanai ne da suke su ne cikakken musabbabi na kamalar dan Adam, wannan kuwa domin suna kunshe da abin da masu Ilimin Usul suke cewa da "Almuktadhi" wato samun yiwuwar abu. Sannan da karin kuma cewa babu wani abu da zai zo ya hana samun kamala sakamakon riko da su, kai sun fi haka ma girmama da daukaka domin su bayanai ne da suke cikakkun sabubba na samun kamalar mutum kan abin ya shafi dukkan sa'adar talikai ba ma dan Adam ba kawai duk suna cikin wannan darasi mai girma na wannan huduba. Domin da an fahimci wannan huduba, aka yi imani da ita, aka kuma yi aiki da ita, da rabauta ta mamaye kowa, da ta kuma game dukkan halittu, rabautar kamalar da daya daga cikin mutane ne ya same ta a kowane zamaninsa, domin shi ne a wancan lokacin aka yi wa wahayi, don haka ake jingina kamalar rabauta gareshi, akwai kuma aljanu da sauran mutane.
Ya kaicon dan Adam! sai ga 'yan fashi (miyagun masu danne gaskiya a daulolin Umayyawa da Abbasawa) a kan hanyar rabautar dan Adam sun kankame ko'ina suna masu hana sautin kira da wilaya ya isa ga dukkan kunnuwa masu sauraro! sai ga dokokin Allah sun cancanza! sai ga 'ya'yan Annabinsa ana karkashewa! sai ga waliyyi Jagoran Muminai an kawar da shi daga fagen lamurran al'umma! sai ga rukunai da bangaye na addini suna rushewa! sai ga dan'adamtaka da mutuntaka ta tafi! rashin mutunci da jahilci sun mamaye! Kimar wahayi ta fadi warwas!.
Sai ga fadin gaskiya ya zama hukuncinsa shi ne cire wuyan mafadinta da halatta dukiyarsa! kuma a kawar da dukkan wata kariya daga gareshi! Sai ga ci gaban Musulunci ya tsaya cik! sai ga shi a yamma an yi gunkin wane ana shi masa albarka cewa yana daga cikin mutanen da suka hana Amir (a.s) sakat, in ba haka ba, da yanzu Jamus da ire-irenta ana shelanta kalmar "Ash'hadu anna muhammadar rasulullah!".
Duba ku gani daga ranar da Ma'aikin Allah (s.a.w) ya shelanta cewa "Duk wanda nake shugabansa to Ali shugabansa ne". Wannan kuwa kusan shekaru dubu da dari hudu ke nan, sai ga shi kiran wilaya ba a ji shi ba sai shekara goma sha tara da suka wuce zuwa ishirin da daya ko sama da haka, kai ko kasa da haka ma, wannan kuwa domin wasu abokai na ba su san Wilaya ko Gadir ba sai shekara biyar zuwa bakwai da suka wuce.
Alhamdulillahi! katangun da 'yan fashi suka gina a kan titi don farautar masu son wucewa zuwa Gadir da wilayar Jagoran muminai (a.s) mun koyi yadda ake haura su, don ni na hango wata 'yar hanya da ta nan na wuce na kuma nuna wa wasu 'yan dubunnan mutane su ma suka haura katangar ta nan, wannan ya sanya wasu 'yan karnukan 'yan fashin da aka tarbiyyantar a kan farauta suka rika yi mini haushi har suka so kona gidajen muminai, suka kwashe mana dukiya kusan shekaru kadan baya da suka wuce zuwa bakwai ke nan. Amma sai muka yi musu gwalo da isgili muka ce mun dai riga mun fahimci Gadir kuma mun haura katangar, kuma koda an kashe mu to farkon digon jinina zai diga ne a matattakalar minbarin manzon rahama (s.a.w) kuma dai dai kasan tafin jagoran muminai (a.s)
Na so a ce ni ne daya daga cikin matakalar minbarin nan da ta samu albarkar hawa kanta da fadin wannan hadisi alhali kafafuwa ba daya ba, ba biyu ba, ba uku ba, kai har kafafu hudu wacce take ta Hasken Allah na farko, da kuma na biyu mai biye masa wanda yake shi ne ainihinsa su ne a kanta.
Wane ne ya isa ya yi bayanin wannan kafafu da tsayuwar su! wane ne ya isa ya yi bayanin hadisan da sirrinsu! kai balle ya je bayanin hannaye masu tsarki da girma wadanda suke kunshe da haske mai dimautar da mai nufin sanin wannan sirri! Wallahi kwakwale sun gajiya su san wannan sirrin! Amma da falalar Ubangijin Talikai da rahamarsa ya ba wa wadannan kwakwale fahimtar sanin ma'anar Harun (a.s) da matsayinsa gun Musa (a.s), kuma ya ba su ikon fahimtar walitaka da Jagorancin muminai, da cewa; babu mai shar'antawa sai waliyyinsa.
Yayin da na yi duba zuwa ga wannan huduba sai na ga cewa; dukkan sakon da Manzon Allah (s.a.w) ya zo da shi yana tattare ciki, muna iya cewa duk rayuwar Manzo (s.a.w) da sauran sako share fage ne ga wannan rana! shi ya sa ma "…Idan ba ka yi ba to ba ka isar da sakonsa ba…" . shi ya sa a kashi na farko zamu ga ta kunshi Kadaita Allah da nuni zuwa ga cewa shar'antawa na Allah ne, yayin da ta kunshi Kadaita Allah da dukkan nau'insa kamar Kadaitakar Hukunci, da Kadaitakar Tafiyar da lamurran bayi, da Kadaitakar Bauta ga Allah, da sauransu.
Sannan domin kada Manzo (s.a.w) ya tsaya ga isar wa mutane sai ya zama shi ne farkon wanda ya yi shaida, kuma ya yi furuci da wilayar Jagorancin Ali (a.s), bayan ya yi furuci da wilayar Ali (a.s) sai ya ci gaba da kawo sababbin bayanai na shari'a, wannan kuwa duk da cewa kafin wannan lokacin ya riga ya yi shimfidarsu kuma ya dasa su tun kafin nan a cikin kwakwalen musulmi, wato an shuka su tun kafin wannan ranar sai dai ranar Gadir ranar girbi ce.
Idan ka so ka ce wannna rana ita ce ranar tafsirin asasin da Kur'ani ya kunsa, ita ce ranar taro, kuma ranar shelanta ma'anonin addini masu kima, kamar ma'anar matsayin Harun (a.s) gun Musa (a.s), da ma'anar wasiyyai kuma halifofi, da ma'anar Babban alkawari mai nauyi da karaminsa, sannan sai karbar bai'a da wasiyyar bin Ali (a.s) da yi masa bai'a suka zama rufe taro.
Wani abin da ya ba ni tsoro shi ne yaya aka samu kungiyar asiri, da aka samu lokacin Manzo (s.a.w) cikin musulmi har Ubangiji ya hana Manzo (s.a.w) ambaton sunan su, kai har ma wahayi yake cewa: "Allah ne yake kare ka daga mutanen…" . Sannan ga ishara da cewa duk siffofin Manzo (s.a.w) suna dabbakuwa a kan Imam Ali (a.s) idan ka cire annabci domin shi ne Harunansa, kuma duk siffofin muminai to shi ne gaba, sannan shiga aljanna ya doru a kan yi masa biyayya, da riko da Jagorancinsa shi da 'ya'yansa, sannan sai ya gargadi mutane game da shugabannin bata da tsoratarwa daga bin su.
A cikin maganganun hikima ya zo cewa; Wadanda suka yi riko da wilaya da jagorancin Ali (a.s) tamkar mala'iku ne da suka yi sujada ga Adam (a.s), amma wadanda suka ki bin sa kamar iblis ne da ya ki yin sujada ga Adam (a.s).
A bangare na karshe na wannan huduba an kawo bayanin wajabcin wasu hukunce-hukunce da suka shafi Salla, Zakka, Halal, Haram, Umarni da Kyakkyawa, da Hani ga Mummuna, wadanda suka lizimci abubuwa daban-daban kamar Tattalin arziki, Zamantakewar al'umma, da makamantansu.
Amma wani abu da yake an yi nuni da shi a nan shi ne; cewar dukkansu suna a matsayin mataccen jiki ne maras rai matukar babu riko da wilaya da jagorancin Ali (a.s), kai hatta da kasawa da gajiyawa a kan riko da jagorancinsa an kira shi da kafirci, haka nan an kira wuce gona da iri kan riko da jagorancinsa da shirka. "Ma fi yawancinsu ba sa imani da Allah sai suna masu shirka" .
Hafiz Muhammad Sa'id
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Zul'hajji,1423 H