Muhammad Bakir
  • Take: Muhammad Bakir
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 14:11:49 1-9-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Muhammad Al-Bakir (a.s) Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Ali dan Husaini dan Ali dan Abi Dalib (a.s). Mahaifiyarsa: Fadima 'yar Hasan (a.s). Alkunyarsa: Abu Ja'afar.
Lakabinsa: Al-bakir da Bakirul Ulum da Asshakir da Al-Hadi. Tarihin haihuwarsa: 1 Rajaba 57 H, ko 3 Safar. Inda aka haife shi: Madina. Matansa: 1-Ummu Farwa 'yar Al-Kasim 2-Ummu Hakim 'yar Asid Assakafiyya 3-4 kuyangi biyu. 'Ya'yansa: 1-Ja'afar Assadik (a.s) 2-Abdullahi 3-Ibrahim 4-Ubaidul-Lahi 5-Ali 6-Zainab 7-Ummu Salama.
Tambarin zobensa: Al-izzatu lil-Lahi.
Tsawon rayuwarsa: Shekara 57. Tsawon Imamancinsa: shekara 19. Sarakunan zamaninsa: Walid dan Abdulmalik da Sulaiman dan Abdulmalik da Umar dan Abdulaziz da Yazid dan Abdulmalik da Hisham dan Abdulmalik.
Tarihin shahadarsa: 7 Zulhajj 114H. Inda ya yi shahada: Madina. Dalilin shahadarsa: Guba da Ibrahim dan Walid dan Yazid ya ba shi a lokacin halifancin Hisham dan Abdulmalik. Inda aka binne shi: Bakiyya a Madina.
Shi ne Muhammad Bakir dan Ali (A.S) kuma babarsa ita ce Fadima 'yar Imam Hasan (A.S) an haife shi a Madina ranar juma'a watan rajab mai alfarma, shekara ta hamsin da biyar, kuma shi ne farkon alawi da aka haifa daga alawiyyawa biyu kuma hashimi tsakanin hashimiyyawa biyu kuma fadimi tsakanin fadimiyyawa biyu, domin shi ne farkon wanda haihuwar imamami biyu ta hadu gareshi. kuma ya yi shahada ta hanyar guba a ranar litinin bakwai ga zulhajji shekara ta dari da goma sha hudu yana da shekaru hamsin da bakwai, kuma dansa Imam Ja'afar Sadik shi ne ya shirya shi ya kuma binne shi a janibin babansa Imam Sajjad (A.S) da kuma ammin babansa kuma kakansa Imam Hasan Mujtaba (A.S) a Bakiyya a Madina.
Ya kasance ma'abocin fifiko mai girma da daukaka da addini da ilimi mai yawa da hakuri mai yalwa da kyawawan halaye da ibada da kaskan da kai da baiwa da rangwame kuma ya kai karshen kyawawan dabi'u wani kirista ya ce masa: kai bakar ne. (wato; saniya)
Sai ya ce: Ni dai Bakir ne.
Sai ya ce: kai dan mai dafa abinci ne.
Sai ya ce: wannan sana'arta kenan.
Sai ya ce: kai dan bakar mace ne ballagaza.
Sai ya ce: idan ka yi gaskiya Allah ya gafarta mata, idan ka yi karya kuma Allah ya gafarta maka.
Sai wannan kirista ya musulunta!
Ya kasance kogi ne a ilimi kamar kumfa mai tunkuda, yana amsa kowace tambaya aka tambaye shi ba tare da tsayawa ba. Ibn Ada Makki yana cewa: Ban taba ganin malamai sun kaskanta a gaban wani mutum ba kamar yadda suke a gaban Bakir (A.S), na ga Hakam bn Utaiba -duk da girmansa- a gabansa kamar wani yaro gaban malaminsa. Muhammad dan Muslim yana cewa: Babu wani abu da ya taba zuwa zuciyata sai da na tambayi Muhammad dan Ali (A.S) har sai da na tambaye shi tambayoyi dubu talatin.
Ya kasance mai yawan ambaton Allah har sai da dansa Imam Ja'afar Sadik (A.S) ya ce: Babana ya kasance mai yawa zikiri, ina tafiya tare da shi amma yana ambaton Allah, kuma ya kasance yana magana da mutane amma wannan ba ya shagaltar da shi daga ambaton Allah . Ya kasance mai yawan tahajjudi da ibada mai yawan kuka da zubar hawaye.