MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
MATSAYIN IMAM RIDHA (a.s) Matsayin Imam Ridha (a.s) Ya zo cewa Imam Musa alKazim (a.s) ya ce wa 'ya'yansa: "Wannan dan'uwanku Ali dan Musa shi ne masanin alayen Muhammad (s.a.w), ku tambaye shi addininku, ku kiyaye abin da yake gaya muku…" .
Imam Ridha (a.s) ya kasance haske ne da ya sauko daga salsalar gidan hasken da ya haskaka wannan duniya, kuma daya daga cikin waliyyan Allah (s.w.t) masu sanar da mutane Ubnagijinsu, masu kama hannayensu zuwa ga shiriya.
Imami (a.s) shi ne wanda yake shiryar da mutane zuwa ga tafarkin tsira bayan wucewar manzon rahama (s.a.w), domin su samu rabauta a duniya da lahira. Don haka kowanne daga cikinsu haske ne da yake haskaka duniya domin mutane suka ga hanyar da zasu taka zuwa ga Ubangiji wanda shi ne kololuwar kamalarsu.
Imami (a.s) ba kawai yana haskaka hanya ba ne, domin wannan duniyar ta taka ta wuce zuwa ga kamala, har ma yana tafiya tare da mutane yana mai kama hannayensu zuwa ga tsira, da kamalar isar cika.
Da wadannan bayanan ne zamu fahimci cewa; babu bambanci garemu a rayuwar Imami (a.s) ya kasance yana halarta cikinmu ko kuwa ba ya halarta, saboda babu bambanci gareshi a wannan yanayin, domin a kowane yanayi yana yin aikinsa na haskaka wa bayin Allah hanyar da zasu bi domin kai wa zuwa ga kamala.
Sai dai wani zai iya cewa me ya sa ba ma ganinsa idan ya faku daga idanuwanmu koda kuwa yana boye a wannan duniyar?
Sai me ce masa: Muna ganin sa mana, sai dai ba ma iya gane shi, kamar dai wani mutum ne da muke gani a hanya mu wuce ba tare da mun kiyaye shi ba, saboda ba mu san shi ba da ma, kuma da za a tambaye mu shi zai yi mana wahala mu gane mun wuce wani mutum, sai dai idan kuwa wani abu ya hada mu da shi ko da kuwa tambayar wani abu ya yi a wurinmu.
Idan muka yi tunanin wannan zamu ga akwai sau da yawa wasu mutane da muke wuce su sau tari, amma ba ma iya gane cewa; muna wuce su saboda ba mu san su ba. Amma da zamu kalli inda suke a kowace rana, mu yi musu sallama, to daga wannan lokacin tunaninmu zai rika lissafa su cikin mutanen da muke da sanayya da su.
A nan ne zamu gane kimar samuwar Imam Mahadi (a.s) a cikinmu, koda kuwa ba ma ganin sa, domin ayyukansa masu muhimmanci ko yana halarta wurinmu ko ba ya halatta wurinmu yana nan yana yin su, akwai kuskure da wasu suke yi na tsammanin cewa; aikinsa yana takaituwa da bayar da taimako ga miskinai, da taimakon wanda ya bace hanya.
A yau cikin fa'idar da muka samu daga karatun Sayyid Allama Kamal Haidari (d.z) ta Irfani mun samu wannan ma'ana madaukakiya a ciki, don haka wannan lamari ne mai daraja da kima a sanin Imami (a.s).
Ba muna kore cewa; Imami (a.s) yana taimakon mutane ne a wurare mabambanta ba, sai dai muna cewa ne; wannan ba shi ne aikinsa na asali ba, don haka yana da kyau mu sanar da duniya hakikanin aikinsa na asali domin a san shi da shi.
Idan da taimakon talakawa, da raunana, da marayu, da marasa galihu ne aikinsa na asali da ma'anar da wasu mutane suke fassarawa, da ayyukan Imam Mahadi (a.s) sun kasance masu karancin kima, da kampanonin Micro Soft, da Rotary Club, da sauran kungiyoyi, hatta da Amurka sun yi alafaharin cewa; ai gudummuwar da muke ba wa duniya ta fi tasa ke nan, domin tasu ana ganin tasirinta a fili.
Don haka aikin Imam Mahadi (a.s) aiki ne mai muhimmanci ba karami ba, ruwayoyi sun nuna cewa: "Da duniya zata yi kwana daya ba tare da Imami daga cikinmu ba, da ta kisfe da mazaunanta…" .
Sa'annan wadannan lakabobi, da muke gani a sunayen wasiyyan manzon Allah (s.a.w) goma sha biyu, ba wasa ba ne, Imam Ridha (a.s) sunan Allah da ya bayyana gareshi ke nan, kamar yadda imamin wannan zamani Imam Mahadi (a.s) ya samu bayyanar wannan suna na mai shiryarwa (a.s) gareshi.
Imam Ridha (a.s) yana da matsayin yardar Allah madaukaki, shi yardajje ne abin yarda, kuma ya kasance wannan yardar tasa ta bayyana a zamaninsa, yayin da ya kasance abin yarda ga kowane abin halitta, sai wanda ya fita daga fidirar halittara ta dan'adamtaka.
Mu sani cewa duk yadda mutum ya kai yabon imamai (a.s) ba zai iya fadin hakikanin abin da yake garesu na matsayi ba, domin wani harshe, ko tunani, ko ilimi, ko dandano, ko hankali, ba zasu iya riskar hakikaninsu ba.
Amincin Allah (s.w.t) ya tabbata gareshi a ranar da aka haife shi, da ranar da ya mutu, da ranar da za a tashe shi.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Tuesday, October 27, 2009