Shahadar Jawad
  • Take: Shahadar Jawad
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 20:26:35 1-10-1403

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
SHAHADAR IMAM MUHAMMAD JAWAD (a.s) SHAHADAR IMAM MUHAMMAD JAWAD (a.s) Wani yakan iya tambayar kansa wai don me wasiyyan manzon Allah (s.a.w) suka fuskanci azabobi a cikin rayuwarsu?
Sai dai idan mutum ya dubu abin da yake faruwa a wannan duniyar a yau zai samu wata amsa mai gamsarwa cikin sauki. Tayiwu wasu abubuwan su buya ga mutum sakamakon idanun zuciyarsa sun makance ba sa gani, ko kuma kunnuwansa sun dode ba sa ji, ko kuma zuciyarsa ta yi tsatsa ta yadda duk yadda aka wanke ta ba ta iya fita.
Idan mun duba sarai zamu ga hadisin nauyaya biyu, ko kuma alkawura biyu da manzon Allah (s.a.w) ya yi wasiyya da su da cewa daya ya fi daya girma, kuma suna tare ba zasu taba rabuwa da shi ba har abada, wadannan su ne littafin Allah da alayensa da yake kiransu da zuriyarsa.
Wannan ruwayar a wancan lokacin tana nufin duk wani wanda ya hau kan mulki ba su ba to ba ya kan shiriya ba ne, kuma duk wani wanda ya yi masa bai'a to ya fadi warwas ya kauce wa hanyar gaskiya. Don haka ne ma muka ga ba su samu sakatawa da wataya ba, sun samu kangi da takunkumi a kowane zamani, a kowane wuri, daga kowane sarki.
Muna gani a yau a siyasar duniya duk wanda aka ce yana mulki kuma ya san ba shi ya ci zabe ba, sannan ya san cewa mutane suna ganin wanda ya ci zaben a matsayin shugaba, suna zuwa gidansa suna taruwa, suna koma masa wurin tambayar makomar kasa, suna bin umarninsa da haninsa a kasa. A wannan yananin babu wani wanda ba shi da amsa kan abin da zai faru na takurawa da kuntatawa tayiwu da kisa ga wancan wanda yake shi ne shugaba na gaskiya.
Idan mun fahimci wannan misali zamu iya gane dalilin da ya sanya wadancan sarakuna takura imamai (a.s) da mabiyansu, da jefa su cikin hadarin rayuwa da nau'o'in takurawa iri-iri. Wannan kuma ya fi wannan misalin na sama karfi, domin wannan yana janibin addini ne da gaskatawa da yarda, da mutane suna ganin ta karkashin wannan imamin ne zasu samu aljanna, kuma da saba masa ne zasu fada wuta.
Don haka ne sai muka ga imam Ali (a.s), da imaman da suka biyo bayansu ba su taba samun lumfasawa daga takurawar masu ikon zamaninsu ba. Sahabban imam Ali (a.s) daya bayan daya aka shayar da su mutuwa ta hannun Mu'awiya, imma da takobi ko guba. Imam Hasan (a.s) kuwa an shayar da shi guba ta hannun matarsa da aka saya ne, shi kuwa imam Husain (a.s) al'amarin shahadarsa a karbala da shi da duk wani wanda yake tare da shi na sahabbansa da ragowar zuriyar manzon Allah (s.a.w) da suke tare da shi ba boyayye ba ne.
Wannan lamarin ya sanya imamai (a.s) sun sauya matakai a zamuna daban-dabank, ba don komai ba sai domin su isar da sakon da manzon Allah (s.a.w) ya bari, wanda wannan lamarin yana daga cikin ayyukansu bayan wucewar annabi (s.a.w). Sai imam Ali Sajjad (a.s) ya isar da sakon musulunci cikin addu'o'I, imam Muhammad Bakir ya bude kofarsa don a samu ilimi, imam Ja'afar Sadik (a.s) ya bude bayar da ilimi ta hannun bude makarantu, imam Musa Kazim ya ci gaba, sai dai ya rayu a gidan sarkar sarki Harun saboda kawai ganin duniya ta karkata garesu a wani karon.
Fushin mutanen duniya game da wulakancin da imam Kazim ya sha ne a kurkuku ya sanya Abdullah Ma'amun dan Harun ya canja salonsa, sai ya kusanto da Imam Ali Ridha dan Musa (a.s) ya sanya shi mai jiran gado da karfin tsiya domin ya kashe wancan fushi na al'umma da ya taso sakamakon wulakancin da ake yi wa zuriyar manzon Allah da al'ummar musulmi ta yarda da fifikonsu. Wani abin mamaki hatta da wanda bai karbi jagorancinsu amma ya yarda da fifikonsu a ilimi da takawa da dukkan wata kamala.
Sai Ma'amun ya yi amfani da makircinsa ya kusanto da imam Ali Ridha (a.s) ya sanya shi mai jiran gado, domin ya kashe shi cikin sauki ta hanyar da ba zata tayar da fushin al'umma ba. Ma'amun shi ya nika gubar da ya ba wa imam Ridha da hannunsa ya sha, amma sai ga shi ya fito masallaci yana kuka, kuma duniyar musulmi ta rika yi masa jaje.
Domin dai mamun ya sake lullube wannanbarna tasa sai ya aura wa imami mai biye wa babansa Ridha (a.s), wato imam Muhammad Jawad dan imam Ali Ridha (a.s) 'yarsa. Amma wannan Ifiritu mai girman kai ya yi haka ne domin ya kashe wannan tsatso mai tsarki, sai ya sanya 'yarsa ta ba wa imam Muhammad Jawad guba, da wannan ne ya kashe uba da da (a.s).
Kada mu manta cewa; dukkan wadannan bayin Allah (a.s) an kashe su ne a hannun sarakunan zamaninsu, babu wani dayansu da ya mutu da kansa. Imma dai wani an kashe shi da takobi kamar imam Ali (a.s) da dansa imam Hasan (a.s), ko kuma an kashe shi da guba kamar sauran wadanda muka ambata a sama. Kuma kowannensu an kashe shi ne sakamakon karkatar da mutane suka yi zuwa ga shiriyarsa, a matsayinsa na wanda ya gaji ilimin annabi (a.s) da nassin addini.
Sai dai maganar yau ta saba da ta da, a da masu mulki suna ganin hadarin alayen manzon Allah (s.a.w) ne saboda suna ganin su ne aka yi nassi a hadisin manzon Allah (s.a.w) da jagorancinsu. Amma a yau masu gaba da wannan gida da mabiyansu saboda sun gaji wancan gabar da ake yi da su ne ta hannun sarakuna.
Sarakuna ba su zauna haka nan ba kawai suka sanya ido wajen ganin sun hana wasiyyar manzon Allah (s.a.w) tabbata, kamar yadda kuskure ne mu dauka cewa sun takaita da sanya makami ko guba kawai. Sun yi abin da ya fi haka muni ne, domin sun sanya malaman fada su kirkiro musu hadisan karya domin gyara musu barnar da suke yi.
Imamai sun sani cewa; babu wani a cikinsu da zai mike ya yi yaki da daula sai an kashe shi, manzon Allah ya riga ya tabbatar musu cewa; imam Husain (a.s) ne zai yi wannan tashin a kashe shi saboda wata hikima a cikin zubar da jininsa. Amma bayan shi wanda zai tashi ya mallaki wannan duniyar shi ne imam Mahadi (a.s).
Don haka ne suka shagaltu da yakar malaman fada ta hanyar bayar da ilimi ingantacce, sai dai malaman fada sun yi kokarin kawar da mafi yawan al'ummar musulmi daga sanin hakikanin gaskiya. Muna ganin yadda imam Ali sajjad (a.s) ya yi wa Zuhuri nasiha, kamar yadda zamu samu irin wannan ga wasu imamai, da kuma umarni da nisantar malaman karya da suke kawar da al'umma daga hanya.
Imamai sun fuskanci wahalhalu daga malamai masu son rai fiye da yadda suka fuskanta daga sarakunan da suke gaba da su. Don haka ne suka yi kokarin sun bayar da ilimi da gadar da shi ga malamai masu gaskiya, domin ya ci gaba kada ya tozarta bayan boyuwar imami wasiyyin annabi (s.a.w) na goma sha biyu imam Mahadi (a.s). Kamar yadda ya yi wasiyya da riko da malami masana iliminsu, masu kiyaye shi har lokacin bayyanarsa.
Wannan gabar da malaman fada suka yi da gidan manzon Allah a cikin ilimi abin takaici ta yadu a duniya matuka, gaba ce wacce mutum ba ya gane ta da wuri, domin ba ta futowa karara ta yi gaba da alayen annabi (s.a.w), amma zata duba me sarki yake so, sai su ce da ma shi ne addini, kuma a kirkiro masa hadisi kan hakan. Ko kuma su duba su ga mece ce falalar Ahlul Baiti (a.s), sai ko su boye ta, ko su ba wa wani mai gaba da alayen manzon Allah (s.a.w) irinta, ko kuma su kirkiri hadisai da suka saba da fatawar da Ahlul Baiti (a.s) suke bayarwa.
A nan zamu yi nuni da rayuwar imam Jawad (a.s) a takaice kamar haka:
Shi ne: Muhammad dan Ali dan Musa dan Ja'afar dan Muhammad dan Ali dan Husain dan Aliyyu bn Abi Dalib (a.s).
An haifi Imam Muhammad al-Jawad (a.s) a Madina a shekara ta (190 bayan hijira).
Ya karbi Imamanci bayan rasuwar mahaifinsa Imam Ali Arridha (a.s) a shekara ta (202 bayan hijira).
Ma'amun ya kai shi Bagdad a lokacin da mahaifinsa Imam Ridha (a.s) ya rasu saboda wadannan dalilai masu zuwa:
1. Domin ya saka Imam Jawad (a.s) a cikin tsaronsa shi da kansa.
2. Domin ya karkato da mabiyan Imam Jawad (a.s) ya aminta daga matsayinsu na yin kiyayya da mulkin Abbasiyawa.
Kusantawar da Ma'amun ya yi wa Imam Jawad (a.s) ta motsa masu kare Abbasiyawa, sai suka dauki matakin kiyayya da shi. kuma suka yi kokarin yin batanci ga Imam Jawad (a.s). Sai suka haifar da shubuhohi a game da Imamancinsa, saboda shi mai karancin shekaru ne.
Sai dai cewa Ma'amun ya kiraye su da su yi kokarin fito da hakikanin Imam Jawad (a.s) ga mutane, idan ya kasance kamar yadda suke fada ne a game da shi cewa babu cancantar Imamanci a tare da shi, to sun zage shi a gaban jama'a. Idan kuma ya zamana cewar yana da sharuddan Imamanci, to sai su kame daga tayar da shubuhohi da kokwanto a kan Imamancinsa.
Sai aka shirya tarurruka saboda hakan, manyan masanan shari'ar Musulunci a wancan zamanin irin su: Yahaya bn Aksam, sun halarci tarurrukan, domin tattaunawa da Imam al-jawad (a.s).
A cikin tarurrukan an tattauna mas'aloli masu girma daga cikin mas'alolin shari'ar Musulunci mafi muhimmanci. Sai sakamakon wadannan tarurrukan ya kasance nasarar Imam Jawad (a.s) da fifikonsa a kan malaman, a cikin gaba dayan abin da aka kawo na mas'aloli. Wannan lamarin ya bayyana wa musulmai cikakkiyar cancantar Imam Jawad (a.s) da Imamancin da ya kasance a kai, da kuma cancantarsa ta shari'a dangane da halifanci.
Sannan Imam Jawad (a.s) ya koma Madina bayan ya yi aikin Hajji ya ci gaba da zama a cikinta har ya zuwa rasuwar Ma'amun.
A lokacin da Ma'amun ya mutu kuma dan'uwansa Mu'utasim ya maye gurbinsa, dan'uwan nasa ya Kirayi Imam Jawad (a.s) a karo na biyu zuwa Bagdad.
Imam Jawad (a.s) ya ci gaba da zama a Bagdad har ya zuwa karshen shekarar da ya isa garin. Sai Mu'utasim ya yi makircinsa na sanya 'yan Ma'amun ta sanya wa Imam Jawad (a.s) guba, al'amarin da ya yi sanadiyyar ransa, wannan ya faru ne a shekara ta (220 bayan hijira).
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Wednesday, November 04, 2009