Manzon Allah
  • Take: Manzon Allah
  • marubucin: Hafiz Muhammad Said
  • Source:
  • Ranar Saki: 19:33:46 1-10-1403

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
MANZON ALLAH MUHAMMAD (s.a.w)
Manzo Muhammad Al-Habib Dan Abdullahi
Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Abdullahi dan Abdul mudallibi dan Hashimi dan Abdu manafi dan Kusayyi dan Kilabi, nasabarsa madaukakiya tana tukewa zuwa ga Annabi Ibrahim (a.s).
Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu 'yar wahabi dan Abdu Manafi dan Zuhrata dan Kilabi.
Alkunyarsa: Abul Kasim, Abu Ibrahim.
Lakabinsa: Almusdafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu.
Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata. Wurin haihuwarsa: Makka. Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana dan shekara arba'in.
Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan'uwantaka da rangwame na gaba daya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karba daga gare shi.
Mu'ujizozinsa: Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce Kur'ani amma wadanda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a boye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma. Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan Rabi'ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.
Yakokinsa: Allah ya yi wa Manzo izinin yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.
Matansa: KHadija 'yar Khuwailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu 'yar Zami'a da A'isha 'yar Abubakar da Gaziyya 'yar Dudan (Ummu Sharik) da Hafsa yar Umar da Ramla 'yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama 'yar Abu Umayya da Zainab 'yar Jahash da Zainab 'yar Huzaima da Maimuna 'yar Al-Haris da Juwairiyya 'yar Al-Haris da Safiyya 'yar Huyayyi dan Akhdabl.
'Ya'yansa: 1-Abdullah 2-Al-Kasim 3-Ibrahim 4-Fadima (a.s) a wani kaulin da Zainab da Rukayya da Ummu Kulsum.
Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan AbdulMudallib ne: Al-haris da Zubair da Abu Dalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-mukawwam da Abu Lahab da Abbas.
Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Amima da Ummu Hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa.
Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirulmuminina Ali dan Abi Dalib (a.s) da Hasan dan Ali da Husain dan Ali da Aliyyu dan Husaini da Muhammad dan Ali da Ja'afar dan Muhammad da Musa dan Ja'afar da Ali dan Musa da Muhammad dan Ali da Ali dan Muhammad da Alhasan dan Ali da Muhammad dan Hasan Mahadi (a.s).
Mai tsaron kofarsa: Anas dan Malik. Mawakinsa: Hassan dan Sabit, da Abdullahi dan Rawahata, da Ka'abu dan Malik.
Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da Abdullahi dan Ummu Maktum da Sa'ad Al-kirdi.
Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!
Tsawon rayuwarsa: shekaru 63. Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23. Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H. Wajan da ya yi wafati: Madina. Inda aka binne shi: Madina a Masallaci Madaukaki Mai alfarma.
Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne karshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa kiyama kuma ita kadai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa karshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi kadai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki daya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W):
Shi ne Muhammad dan Abdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makka ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan bollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).
Aiko Annabi Mai Daraja (S.A.W)
An aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da sako a 27 ga Rajab bayan yana dan shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaki .
Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sakon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta" .
A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka rika yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni" .
Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane kalilan, na farkonsu Imam Ali sannan sai matarsa Hadiza (A.S) sannan sai wasu mutane.
Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S).
Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai karfinsu ya dadu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa mai sauki mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har suka fi dukkan duniya da addini na sama da wadanda ba na sama ba.
Kuma an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba.
Mutuwa Mai Zafin Gaske
Tun lokacin da aka aiko Annabi da sako har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Kur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a hada shi kamar yadda yake a yau din nan.
Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.
Bayan cikar addini da kafa Ali dan Abu Dalib (A.S) shugaba na al'umma kuma halifa bayan Annabi (S.A.W) wannan kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana sai Allah ya saukar da ayar: "A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni'imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini" . Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauki, sai dai ya yi tsanani har sai da ya hadu da Ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H.
Kuma wasiyyinsa halifansa Imam Ali (A.S) shi ne ya yi masa wanka da salla da binne shi a dakinsa a Madina inda kabarinsa yake yanzu.
Ya kansace abin koyi ne shi a rikon amana da ikhlasi da gaskiya da cika alkawari da kyawawan halaye, da girma, da kyawawna dabi'u, da baiwa, da ilmi, da hakuri, da rangawame, da afuwa, da sadaukantaka, da tsentseni, da takawa, da zuhudu, da baiwa, da adalci, da kaskan da kai, da jihadi.
Jikinsa ya kasance kololuwa wajen kyau da kuma daidaito da dacewa, kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye da ladabi da dabi'a kuma sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.
Atakaice, ya tattara dukkan wata dabi'a mai kyau da girma da daukaka da kuma ilimi da adalci da takawa da kuma iya tafiyar da al'amuran duniya da na lahira, wadanda babu wani mahaluki da yake da irinsu.
Wannan shi ne annabin musulmi kuma wannan shi ne addinin musulunci, kuma addininsa shi ne mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai domin shi: "Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo" .